Jam’iyyar APC ta kawo kujeru 25 na Majalisar Dokoki a Kogi

Jam’iyyar APC ta kawo kujeru 25 na Majalisar Dokoki a Kogi

Mun samu labari daga Daily Trust cewa dubban Magoya bayan APC sun kidime da farin-ciki bayan an samu labari cewa jam’iyyar APC mai mulki ce tayi nasara a zaben majalisar dokoki a Kogi.

Jam’iyyar APC ta lashe kaf kujerun majalisar dokokin da ke jihar Kogi a zaben da aka karasa shekaran jiya Asabar 23 ga Watan Maris. APC ta kafa tarihin kawo dukannin kujerun ‘yan majalisar dokoki na jihar a zaben wannan karo.

A da can an sanar da cewa APC ta lashe kujeru 23 cikin 25 da ake da su a majalisar dokoki na jihar inda aka dakatar da zaben Lokoja I da kuma shiyyar Igalamela-Odolu. Zaben cike-gibi da aka yi yanzu ya nuna APC ta ci duka kujerun.

KU KARANTA: Abba Gida-gida ya yi watsi da sakamakon zaben gwamnan Kano

Jam’iyyar APC ta kawo kujeru 25 na Majalisar Dokoki a Kogi
Kujerun ‘Yan Majalisar Kogi su na hannun Jam’iyyar APC
Asali: Facebook

A zaben majalisar tarayya dai idan ba a manta ba, APC ta samu kujerar Sanatoci 2, yayin da PDP ta ci 1. Haka kuma a majalisar wakilai, jam’iyyar APC mai mulki ta lashe kujeru 7 a cikin ‘yan majalisar tarayya 9 da ake da su a jihar.

Darekta Janar na yakin neman zaben APC a jihar ta Kogi wayau Cif David Onoja yayi magana game da wannan nasara da su ka samu a zaben na 2019 inda yace kama-karyar PDP shi ya jawo masu faduwa babban zaben na bana.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel