APC ta yi watsi da sakamakon zaben gwamnan Benue, ta doshi kotu

APC ta yi watsi da sakamakon zaben gwamnan Benue, ta doshi kotu

- Jam’iyyar APC reshen jihar Benue, ta yi watsi da sakamakon zaben gwamnan da aka kaddamar Gwamna Samuel Ortom na jam’iyyar PDP a matsayin wanda yayi nasara

- Ortom ya samu kuri’u 434,473 inda ya kayar da babban abokin adawarsa, Emmanuel Jime na APC, wanda ya samu kuri’u 345,155

- Eugene Aliegba, sakataren kungiyar kamfen din Jime/Ode, ya bayyana cewa jam’iyyar APC za ta kalubalanci sakamakon a kotu

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Benue, ta yi watsi da sakamakon zaben gwamnan da aka kaddamar a ranar Lahadi, 24 ga watan Maris, inda aka bayyana Gwamna Samuel Ortom na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a matsayin wanda yayi nasara.

A wani jawabi da jam’iyyar ta saki a ranar Lahadi, 24 ga watan Maris, a Makurdi ta bayyana cewa sakamakon bai nuna burin mutane ba.

APC ta yi watsi da sakamakon zaben gwamnan Benue ta doshi kotu
APC ta yi watsi da sakamakon zaben gwamnan Benue ta doshi kotu
Asali: UGC

Jawabin dauke da sa hannun Eugene Aliegba, sakataren kungiyar kamfen din Jime/Ode, ya bayyana cewa jam’iyyar APC za ta kalubalanci sakamakon a kotu.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), ta kaddamar da Ortom a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna da kuma zaben da aka gudanarwa a ranar 9 ga watan Maris da kuma 23 ga watan Maris.

KU KARANTA KUMA: Masu cewa da Atiku kar ya tafi Kotu, mutanen banza ne – Obasanjo

Ortom ya samu kuri’u 434,473 inda ya kayar da babban abokin adawarsa, Emmanuel Jime na APC, wanda ya samu kuri’u 345,155.

Sanarwar ya kaddamar da cewa ko kadan APC bata amince da sakamakon zaben ba. Sannan ta yi godiya ga wadanda suka zabi Jime da Sam Ode, yan takarar gwamna da mataimakin gwamna na jam’iyyar a zaben.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel