Ba zamu yarda ba, mu hadu a kotu - Abba Gida-gida ya yi watsi da sakamakon zaben gwamnan Kano

Ba zamu yarda ba, mu hadu a kotu - Abba Gida-gida ya yi watsi da sakamakon zaben gwamnan Kano

Dan takarar jam'iyyar PDP a zaben kujerar gwamnan jihar Kano da aka kammala, Abba Kabir Yusuf, ya yi watsi da sakamakon zaben da hukumar zabe ta kasa (INEC) ta sanar bayan kammala tattara sakamakon zabe a zagaye na biyu da aka yi a wasu mazabu dake fadin kananan hukumomin 28.

Dakta Abdulahi Umar Ganduje, gwamnan jihar Kano kuma dan takarar jam'iyyar APC a zaben gwamna, ya sake lashe zabe a karo na biyu bayan an kai ruwa rana tsakaninsa da dan takarar jam'iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf.

Ganduje ya lashe zaben ne da banbancin kuri'u 9,000 bayan cike gurbin kuri'un da Abba ya dora masa a zagayen farko na zaben da aka yi a ranar 9 ga watan Maris.

Sai dai, a sakon da ya fitar a shafin sa na Tuwita (govAbbakabir), Abba ya ce, "jam'iyyar mu ta PDP tayi watsi da sakamakon zaben da hukumar zabe ta kasa ta sanar a jihar da yammacin ranar Lahadi.

"Mu hadu a kotu. Zamu tabbatar da cewar adalci da dimokradiyya sun yi nasara duk rintsi, zamu karbo nasarar mu da aka kwace.

Ba zamu yarda ba, mu hadu a kotu - Abba Gida-gida ya yi watsi da sakamakon zaben gwamnan Kano
Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

A sakamako na karshe da INEC ta sanar bayan an hada sakamako daga zaben farko da na biyu da aka gudanar, jam'iyyar APC na da kuri'u 1,033,695 da suka ba ta nasara a kan jam'iyyar PDP, wacce ta samu kuri'u 1,024,713.

A baya Legit.ng ta sanar da ku cewar wakilan jam'iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Kano da aka kammala bayan tattara sakamakon zaben zagaye na biyu sun ki saka hannu a kan sakamakon da baturen zabe, Farfesa Bello Shehu, ya sanar a Kano.

DUBA WANNAN: Kotu ta bayyana yadda INEC ta canja sakamakon zaben gwamna a Osun

Da ya ke magana bayan kammala tattara sakamakon, mukaddashin shugaban jam'iyyar PDP a jihar Kano, Rabi'u Suleiman Bichi, ya yi korafin cewar an kitsa sakamakon zaben ne kawi domin ba a gudanar da zabe a jiya, Asabar, 23 ga watan Maris.

Kazalika, mamba a majalisar wakilai daga karamar hukumar Dala, Aliyu Sani Madakin Gini, ya yi korafin cewar 'yan daba sun tayar da hargitsi da ya hana jama'a kada kuri'a a mazabar Gama.

Da ya ke mayar da martani a kan abinda wakilan na PDP suka yi, sanatan jihar Kano ta Arewa, Barau Jibrin, ya ce duk mai wani korafi ya nufi kotu domin shigar da korafin sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel