Wakilan jam'iyyar PDP a Kano sun ki rattaba hannu a kan sakamakon zabe

Wakilan jam'iyyar PDP a Kano sun ki rattaba hannu a kan sakamakon zabe

Wakilan jam'iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Kano da aka kammala bayan tattara sakamakon zaben zagaye na biyu sun ki saka hannu a kan sakamakon da baturen zabe, Farfesa Bello Shehu, ya sanar a Kano.

Da ya ke magana bayan kammala tattara sakamakon, mukaddashin shugaban jam'iyyar PDP a jihar Kano, Rabi'u Suleiman Bichi, ya yi korafin cewar an kitsa sakamakon zaben ne kawi domin ba a gudanar da zabe a jiya, Asabar, 23 ga watan Maris.

Kazalika, mamba a majalisar wakilai daga karamar hukumar Dala, Aliyu Sani Madakin Gini, ya yi korafin cewar 'yan daba sun tayar da hargitsi da ya hana jama'a kada kuri'a a mazabar Gama.

Da ya ke mayar da martani a kan abinda wakilan na PDP suka yi, sanatan jihar Kano ta Arewa, Barau Jibrin, ya ce duk mai wani korafi ya nufi kotu domin shigar da korafin sa.

Wakilan jam'iyyar PDP a Kano sun ki rattaba hannu a kan sakamakon zabe
Wata cibiyar tattara sakamakon zabe a Kano
Asali: Twitter

A cewar sa, "an fara tattara sakamakon zaben ne tun daga matakin mazabu zuwa kananan hukumomi inda ya kamata a yi duk wani korafi, amma ba a cibiyar tattara sakamako ta jiha ba bayan wakilan mazabu da kananan hukumomi sun amince da sakamakon ba."

A sakamakon zaben na jihar Kano, Dakta Abdulahi Umar Ganduje, gwamnan mai ci kuma dan takarar jam'iyyar APC a zaben gwamna, ya sake lashe zabe a karo na biyu bayan an kai ruwa rana tsakaninsa da dan takarar jam'iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf.

DUBA WANNAN: Tambuwal ya sake lashe zaben gwamna a jihar Sokoto

Ganduje ya lashe zaben ne da banbancin kuri'u 9,000 bayan cike gurbin kuri'un da Abba ya dora masa a zagayen farko na zaben da aka yi a ranar 9 ga watan Maris.

Sakamakon kananan hukumomi biyu ya kawo tsaiko wajen sanar da sakamakon zaben. Kananan hukumomin su ne; Kibiya da Nasarawa.

A karamar hukumar Kibiya, Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 228, yayin da Abdullahi Umar Ganduje na jam'iyyar APC ya samu kuri'u 371.

A karamar hukumar Nasarawa, APC ta samu adadain kuri'u 10,536, yayin da jam'iyyar PDP ta samu adadin kuri'u 3,409.

Yanzu bayan kammala wa tare da hada jimillar dukkan kuri'un kowacce jam'iyya daga zabukan biyu da aka gudanar, jam'iyyar APC na da kuri'u 1,033,695 da suka ba ta nasara a kan jam'iyyar PDP, wacce ta samu kuri'u 1,024,713.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel