Bayan an kai ruwa rana: Ganduje ya lashe zaben gwamna a Kano, INEC ta sanar

Bayan an kai ruwa rana: Ganduje ya lashe zaben gwamna a Kano, INEC ta sanar

Dakta Abdulahi Umar Ganduje, gwamnan jihar Kano kuma dan takarar jam'iyyar APC a zaben gwamna, ya sake lashe zabe a karo na biyu bayan an kai ruwa rana tsakaninsa da dan takarar jam'iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf.

Ganduje ya lashe zaben ne da banbancin kuri'u 9,000 bayan cike gurbin kuri'un da Abba ya dora masa a zagayen farko na zaben da aka yi a ranar 9 ga watan Maris.

Sakamakon kananan hukumomi biyu ya kawo tsaiko wajen sanar da sakamakon zaben. Kananan hukumomin su ne; Kibiya da Nasarawa.

A karamar hukumar Kibiya, Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 228, yayin da Abdullahi Umar Ganduje na jam'iyyar APC ya samu kuri'u 371.

A karamar hukumar Nasarawa, APC ta samu adadain kuri'u 10,536, yayin da jam'iyyar PDP ta samu adadin kuri'u 3,409.

Da dumin sa: Ganduje ya lashe zaben gwamana a Kano
Ganduje ya lashe zaben gwamana a Kano
Asali: Twitter

A karshen zaben raba gardama da aka kammala jiya, Asabar, a kananan hukumomi 28, APC ta samu jimillar kuri'u 45,876 da suka ba ta rinjaye a kan jam'iyyar PDP wacce ta samu jimillar kuri'u 10,239.

DUBA WANNAN: Tambuwal ya sake lashe zaben gwamna a jihar Sokoto

A zaben ranar Asabar, 9 ga watan Maris, da hukumar zabe ta kasa (INEC) ta bayyana cewar bai kammalu ba, jam'iyyar PDP ce ke kan gaba da adadin kuri'u 1,014,474, yayin da jam'iyyar APC ke da adadin kuri'u 987,817.

Yanzu bayan kammala wa tare da hada jimillar dukkan kuri'un kowacce jam'iyya daga zabukan biyu da aka gudanar, jam'iyyar APC na da kuri'u 1,033,695 da suka ba ta nasara a kan jam'iyyar PDP, wacce ta samu kuri'u 1,024,713.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel