Yanzu yanzu: Yadda gobara mai karfi ta babbake shaguna da wani gida a Kano

Yanzu yanzu: Yadda gobara mai karfi ta babbake shaguna da wani gida a Kano

- Hukumar kwana kwana ta jihar Kano ta ce wata gobara mai karfi ta lakume wani gida a kan titin France da ke daura da bankin Zenith a yankin Sabon Gari

- Mai magana da yawun hukumar, Alhaji Saidu Mohammed, ya ce gobarar ta fara ne da misalin karfe 5:07 na yammacin ranar Asabar, 23 ga watan Maris

- Ya kara da cewa gobarar ta tashi ne sakamakon fashewar ma'ajiyar iskar gas da ke a cikin wani shago da ke hade da gidan

Hukumar kwana kwana ta jihar Kano ta ce wata gobara mai karfi ta lakume wani gida a kan titin France da ke daura da bankin Zenith a yankin Sabon Gari da ke a kwaryar jihar.

Mai magana da yawun hukumar, Alhaji Saidu Mohammed, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, ya ce gobarar ta fara ne da misalin karfe 5:07 na yammacin ranar Asabar, 23 ga watan Maris.

"Mun samu kiran gaggawa daga jami'in rundunar 'yan sanda, Malam Kabiru Umar ( a ranar Asabar) da misalin karfe 5:07 na yamma, cewar gobara ta kama a wani gida mai shaguna a hade da shi.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: PDP ta sha kasa a Ekiti, APC ta lashe kujeru 26 na majalisar jihar

Yanzu yanzu: Yadda gobara mai karfi ta babbake shaguna da wani gida a Kano
Yanzu yanzu: Yadda gobara mai karfi ta babbake shaguna da wani gida a Kano
Asali: Twitter

"Jin wannan labarin ya sa muka gaggauta tura motar kwana kwana zuwa inda gobarar ta kama da misalin karfe 5:18, domin ganin an dakile yaduwar gobarar," a cewarsa.

Ya ce gobarar ta shafi dakuna guda biyar, sai falo da kuma shaguna biyar inda rahotanni suka bayyana cewa shago daya ana sayar da iskar gas.

Ya kara da cewa gobarar ta tashi ne sakamakon fashewar ma'ajiyar iskar gas da ke a cikin shagon.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel