Da duminsa: PDP ta sha kasa a Ekiti, APC ta lashe kujeru 26 na majalisar jihar

Da duminsa: PDP ta sha kasa a Ekiti, APC ta lashe kujeru 26 na majalisar jihar

Rahotannin da Legit.ng Hausa ta samu ya yi nuni da cewa jam'iyyar APC ta lashe dukkanin kujeru 26 na majalisar dokokin jihar Ekiti. A ranar 9 ga watan Maris, 2019 ne aka dakatar da zaben gwamnan jihar da na 'yan majalisun dokoki na jihar.

A ranar 23 ga watan Maris aka gudanar da zaben jihar zagaye na biyu, inda daga bisani Dr. Chika Asokwa, malamin zaben jihar, ya sanar da sakamakon zaben.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: Har yanzu zaben jihar Bauchi bai kammala ba saboda rikicin Tafawa Balewa - INEC

Juwa Adegbuyi na jam'iyyar APC ya samu kuri'u 5,484 da ya bashi damar lallasa Ojoade Fajana na jam'iyyar PDP wanda ya samu kuri'u 3,258.

Da wannan nasara da Adegbuyi ya samu, a yanzu APC na da cikakken iko kan kujeru 26 na majalisar dokokin jihar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel