Da duminsa: Har yanzu zaben jihar Bauchi bai kammala ba saboda rikicin Tafawa Balewa - INEC

Da duminsa: Har yanzu zaben jihar Bauchi bai kammala ba saboda rikicin Tafawa Balewa - INEC

Dan takarar gwamnan jihar Bauchi karkashin jam'iyyar PDP, Sanata Bala Muhammad (Kauran Bauchi) ya samu gagarumar nasara a zaben gwamnan jihar zagaye na biyu da aka gudanar a kananan hukumomi 15 da ke a jihar a ranar Asabar 23 ga watan Maris.

Da ya ke sanar da sakamakon zaben, malamin zaben jihar Farfesa Kyari Muhammad ya bayyana cewa dan takarar PDP ya lashe zaben ne da kuri'u 6376 yayin da dan takarar gwamnan jihar karkashin APC, kuma gwamnan jihar na yanzu, Muhammad Abddulahi Abubakar ya samu kuri'u 5117.

Sai dai Farfesa Kyari Muhammad ya ce hukumar za ta sanar da sakamakon zaben gwamnan jihar bayan an gama sauraren karar da jam'iyyar APC ta shigar kotu kan sakamakon zaben karamar hukumar Tafawa Balewa.

KARANTA WANNAN: Yanzu: APC ta samu kuri'u 5,117 yayin da PDP ke kan gaba da kuri'u 6,376 a Bauchi

Da duminsa: Har yanzu zaben jihar Bauchi bai kammala ba saboda rikicin Tafawa Balewa - INEC
Da duminsa: Har yanzu zaben jihar Bauchi bai kammala ba saboda rikicin Tafawa Balewa - INEC
Asali: Getty Images

A baya Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa gwamnan jihar Bauchi Muhammad Abdullahi Abubakar da jam'iyyar APC a jihar ta shigar da kara a babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Abuja inda ta bukaci kotun ta dakatar da INEC daga ci gaba da karbar sakamakon zaben karamar hukumar Tafawa Balewa, wanda aka soke shi saboda rikicin da hana sanar da sakamakon zaben a cibiyar tattara sakamakon zabe ta karamar hukumar.

Bisa rahotannin da Legit.ng Hausa ta samu ta bakin wakilinta a jihar Sani Hamza Funtua, hukumar zabe ta kammala sanar da sakamakon zaben gwamnan jihar zagaye na biyu.

Jimillar sakamakon zaben Bauchi zagaye na biyu:

APC 5117

PPD. 6376

Banbancin kuri'u 1259

Zaben jihar na farko

APC 465, 453

PDP. 469,512

Banbancin kuri'u. 4509

Jimillar zabukan guda biyu

APC 470,570

PDP. 475,888

Jimillar banbancin kuri'un zabukan guda biyu

5768, PDP ce a kan gaba.

-----------------------------------

SAHIHIN SAKAMAKON ZABE DAGA INEC

-----------------------------------

Jama'are LGA

APC 74

PDP. 54

Valid votes. 128

Rejected votes 0

Total votes cast 128

-----------------------------------

Toro LGA

APC 536

PDP 828

-----------------

Katagum LGA

APC 261

PDP 203

Valid votes 467

Rejected votes 17

Total votes cats 484

Valid votes 715

Rejected votes 33

Total votes cast 748

-----------------------------------

Alkaleri. LGA

APC 264

PDP. 444

Valid votes 715

Rejected votes 33

Total votes cast 748

-----------------------------------

Gamawa LGA

APC 152

PDP 96

Valid votes 250

Rejected votes 05

Total votes cast 255

-----------------------------------

Kirfi LGA

APC. 206

PDP. 473

Valid votes. 691

Rejected votes 35

Total votes cast 726

-----------------------------------

Ningi. LGA

APC 728

PDP 791

Valid votes. 1,549

Rejected votes 79

Total votes cast 1,628

-----------------------------------

Ganjuwa LGA

APC. 432

PDP. 353

Valid votes 785

Rejected votes 18

Total votes cast 803

-----------------------------------

Shira LGA

APC 152

PDP. 86

Valid votes 238

Rejected votes 09

Total votes cast 247

-----------------------------------

Giade LGA

APC 639

PDP. 532

Valid votes 1,176

Rejected votes 33

Total votes cast 1209

-----------------------------------

Itasgadau LGA

APC 421

PDP 619

Valid votes 1044

Rejected Votes 35

Valid votes 1,079

-----------------------------------

Darazo LGA

APC 824

PDP 749

Valid votes 1,599

Rejected votes 36

Total votes cast 1,635

-----------------------------------

Dass LGA

APC 184

PDP. 358

Valid votes 546

Rejected votes. 26

Total votes casted. 572

-----------------------------------

Misau LGA

APC 111

PDP 312

Valid votes 433

Rejected votes 05

Total votes cast 438

-----------------------------------

Bogoro L.G.A

APC 101

PDP. 478

Total valid votes 582

Rejected 25

Total votes cast 607

-----------------------------------

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel