Masu cewa da Atiku kar ya tafi Kotu, mutanen banza ne – Obasanjo

Masu cewa da Atiku kar ya tafi Kotu, mutanen banza ne – Obasanjo

Tsohon shugaban kasar Najeriya Cif Olusegun Obasanjo, yayi tir da wadanda ke adawa da yunkurin Atiku Abubakar na zuwa kotu ya kalubalanci nasarar da shugaba Buhari ya samu a zaben 2019.

Olusegun Obasanjo yace masu neman Atiku Abubakar ya hakura da zuwa kotu, ba mutanen kirki banem inda yace su na neman kawo tashin hankali ne a Najeriya. Obasanjo yayi wannan bayani ne jiya Asabar 23 ga Watan Maris.

Cif Obasanjo ya kuma yi tsokaci game da zaben jihar Osun da kotu ta rusa inda tace ‘Dan takarar PDP, Sanata Ademola Adeleke, ne ainihin wanda ya lashe zaben. Wannan ya sa Obasanjo yake ganin gara Atiku ya sheka gaban kotu.

Obasanjo yayi wannan bayani ne ta bakin wani babban hadimin sa inda yace abu ne mai kyau ace ‘dan takarar shugaban kasar na PDP a zaben bana watau Alhaji Atiku Abubakar ya tafi gaban Alkalai domin a fito masa da hakkin sa.

KU KARANTA: Buhari ya ki bari kowa ya sa-baki cikin nadin sababbin Ministocin sa

Masu cewa da Atiku kar ya tafi Kotu, mutanen banza ne – Obasanjo
Obasanjo ya soki wadanda ke cewa ka da Atiku ya je Kotu
Asali: UGC

Tsohon shugaban kasar yace Nahiyar Afrika da ma Duniya baki daya tana kallon zaben da ake yi a Najeriya. Obasanjo ya yabawa matakin da Ademola Adeleke ya dauka har kuma ya samu nasara a kotu bayan a da ance ya fadi zabe.

Wasu dai su na ta rokon Atiku Abubakar ya fawwalawa Allah lamarin zaben shugaban kasar da aka yi a bana bayan ya sha kashi a hannun jam’iyyar APC. Masu wannan maganar su na ganin dangana zai fi kawo zaman lafiya a Najeriya.

Obasanjo yace duk da ya ki yin magana game da zaben da aka yi, ya zama dole yanzu ya fito yayi magana game da masu neman hana Atiku zuwa Kotu. Obasanjo yace idan har Buhari zai tafi kotu a da, babu abin da zai hana Atiku yin hakan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel