Yanzu-yanzu: PDP ta lashe kujeru 2, APC ta samu daya a karashen zaben birnin tarayya Abuja

Yanzu-yanzu: PDP ta lashe kujeru 2, APC ta samu daya a karashen zaben birnin tarayya Abuja

Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta lashe zaben kananan hukumomi 2 cikin ukun da ya rage ba'a kammala ba a ranar 9 ga watan Maris, 201 yayinda jam'iyyar APC ta samu kujera daya.

PDP ta lashe zaben karamar hukumar Kuje da Bwari, yayinda APC ta lashe na Kwali

A Kuje, baturen zaben, Farfesa Titus Ibekwe, ya alanta Abdullahi Sabo na PDP matsayin zakarar zaben inda ya samu kuri'u 19,090 yayinda Abdullahi Galadima na APC ya samu 15,187.

A Bwari, Baturen zaben, Farfesa Mohammed Umaru, ya alanta Gabaya na PDP matsayin wanda ya lashe zaen inda ya samu kuri'u 31,114 yayinda Musa Dikko na APC ya samu kuri'u 24,137.

A Kwali, Baturen zaben, Farfesa Simon Kawe, ya bayyana Chiya na APC matsayin zakarar zaben da kuri'u 14,245 yayinda Ibrahim Daniel na PDP ya samu kuri'u 14,189.

KU KARANTA: Boko Haram: Shugaban kasa ya sallami manyan hafsoshin tsaro sakamakon kisan soji 23

A yanzu haka, jam'iyyar APC ta kwashe kujeru hudu cikin shida na kananan hukumomin birnin tarayya Abuja inda PDP ta samu biyu.

A bayan mun kawo muku cewa Jam'iyyar All Progressives Congress ta lashe dukkan kananan hukumomi uku da aka sanar ranar 9 ga watan Maris.

Gwagwalada

Mustapha Adamu Danza (APC) - 21,960

Abubakar Giri (SDP) - 14,105

AMAC

Abdullahi Adamu Candido (APC) - 53,753

Vivian Anazodo (PDP) - 35,753

Abaji

Abdulrahman Ajiya (APC) - 13,442

Muhammad Ashafa (APC) - 10,473

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel