Shugaba Buhari zai fitar da sababbin Ministocin Najeriya a kasar waje

Shugaba Buhari zai fitar da sababbin Ministocin Najeriya a kasar waje

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai fitar da jeringiyar Ministocin Najeriya a lokacin da ya bar kasar ya tafi kasar waje domin ya huta. Daily Trust ta rahoto wannan a jiya Asabar 23 ga Watan Maris.

Jaridar tace ta samu labari daga majiya mai karfi cewa shugaban kasar zai zauna ya fitar da wadanda za su zama Minista a gwamnatin sa wannan karo a lokacin da ya bar Najeriya. Ana tunani kwanan nan Buhari zai tafi hutu kasar waje.

Shugaba Buhari zai sanar da majalisar dattawa da ta wakilai game da wannan hutu da zai dauka inda a wannan lokacin zai bar mataimakin sa watau Yemi Osinbajo ya cigaba da jan ragamar mulkin kasar har sai ya samu dawowa gida.

KU KARANTA: APC ta lashe kujeru 65 yayin da PDP ta samu Sanatoci 41

Shugaba Buhari zai fitar da sababbin Ministocin Najeriya a kasar waje
Buhari zai yi aikin sunayen Ministoci a kasar waje bayan ya ki bari ayi masa katsalandan
Asali: Facebook

A halin yanzu shugaban kasar bai son jin labarin wani ya zo neman alfarma domin a sa sunan wani a cikin jerin Ministocin kasar. Wannan ya sa zai bar Najeriya domin ya samu yayi wannan aiki ba tare da wasu sun tsoma masa baki a ciki ba.

Kusa bisa dukkan alamu, a wannan karo shugaba Buhari zai zarce kwanaki 10 a kasar waje kamar yadda ya saba idan ya tafi shakatawa. Majiyar tace shugaban kasar zai tsaya a waje yayi wasu abubuwan da ke gaban sa kafin ya dawo gida.

A 2015, shugaba Buhari ya dauki watanni 6 kafin ya iya kafa gwamnati. A bana ana tunanin cewa ba za a jima irin haka ba. Wani da ke fadar shugaban kasar yace ana kyautata zaton a tura sunayen Ministoci da zarar an kafa sabuwar majalisa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel