Dalilin da yasa har yanzu bamu sanar da sakamakon zaben gwamnan Bauchi ba - INEC

Dalilin da yasa har yanzu bamu sanar da sakamakon zaben gwamnan Bauchi ba - INEC

Batun sanar da sakamakon zaben raba gardama a jihar Bauchi ya dauki wani sabon salo bayan kwamishinan hukumar zabe ta kasa (INEC), Ibrahim Abdullahi, ya sanar da cewar har yanzu baturen zaben gwamnan jihar, Farfesa Kyari Mohammed, bai iso ma jihar ba.

An gudanar da zaben raba gardamar ne a akwatinan zabe 36 dake mazabu 29 a kananan hukumomi 20 na jihar Bauchi, sai dai rashin sanar da sakamakon zaben da aka kammala tun jiya na cigaba da haifar da zulumi a zukatan mutane.

Abdullahi ya yi kira ga jama'a da su yi watsi da jita-jitar cewar akwai shirin canja sakamakon zaben domin bawa jam'iyyar APC damar yin nasara.

Da yake magana da manema labarai da misalin karfe 1:20 na safiyar yau, Lahadi, Abdullahi ya ce, "akwai bukatar na gana da ku domin ku sanar da jama'a cewar kar su dogara da maganganun dake yawo a dandalin sada zumunta cewar za a canja salamakon zabe.

Dalilin da yasa har yanzu bamu sanar da sakamakon zaben gwamnan Bauchi ba - INEC
Cibiyar INEC ta tattara sakamako a Bauchi
Asali: UGC

"INEC ba ta da wani bangare da take son ya lashe zabe. Tsarin da muke amfani da shi na sanar da sakamakon zabe tun daga rumfunan zabe ba zai bayar da damar canja sakamakon zabe ba daga baya, musamman a irin wannan lokaci da labari ba ya wuyar kewaya wa.

DUBA WANNAN: Kotu ta bayyana yadda INEC ta canja sakamakon zaben gwamna a Osun

"Tuni an kawo dukkan sakamakon zabe daga kananan hukumomi 15, su na hedikwatar hukumar zabe dake Bauchi. Jama'a su yi hakuri yayin da muke jiran isowar baturen zabe."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel