Mayakan Boko Haram sun kashe Mutane 7 a Diffa

Mayakan Boko Haram sun kashe Mutane 7 a Diffa

Kimanin rayukan mutane bakwai sun salwanta yayin aukuwar wani mummunan hari na kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram Kudu maso Gabashin kasar Nijar daura da iyaka ta kasar Najeriya.

Kungiyar masu ta'adar sun kai hari na kwanton bauna har kashi uku a daren ranar Asabar a yankin Diffa na kasar Nijar da ke gab da iyaka ta kasar Najeriya a yankin ta na Arewa maso Gabas kamar yadda hukomomi suka bayyana.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, aukuwar wannan mummunan hari ta salwantar da rayukan mutane bakwai ba ya ga awon gaba da wasu mata biyu da kuma kone kasuwa da kuma muhallai da dama na al'umma.

Mayakan Boko Haram sun kashe Mutane 7 a Diffa
Mayakan Boko Haram sun kashe Mutane 7 a Diffa
Asali: Twitter

Wata majiyar rahoto da ta wallafa a shafin ta na sada zumunta, Alternative Espace Citoyen ta ce, hare-haren da su ka auku kashi hudu sun yi sanadiyar salwantar da rayukan mutane 11 da tuni suka riga mu gidan gaskiya.

A ranar Alhamis ta makon da ya gabata, wani hari na Mayakan Boko Haram a kauyen Karidi da ke kan iyaka ta kasar Najeriya ya salwantar da rayukan mutane takwas da suka hadar da Mace guda.

A ranar 9 ga watan Maris, wani mummunan hari na Mayakan Boko Haram ya salwantar da rayukan Dakarun soji 9 na kasar Nijar a kauyen na Karidi. Kazalika rayukan soji 7 sun salwanta yayin aukuwar wani hari a iyakar Najeriya cikin watan da ya gabace mu.

KARANTA KUMA: Atiku ya taya Gwamna Tambuwal murnar samun nasara

A kwana-kwanan nan yankin Diffa da ke kan iyaka ta kasar Najeriya a yankin ta na Arewa maso Gabas, ya fuskanci barazana ta munanan hare-hare, inda rayukan 'yan ta'dda kimanin 33 suka salwanta yayin mayar da martani na hukumomin tsaro.

An yi itifakin cewa, kawowa yanzu rayukan kimanin Mutane 27,000 sun salwanta tare da asarar muhallai na fiye da Mutane Miliyan biyu tun yayin da ta'addancin kungiyar Boko Haram ya kunno kai a shekarar 2009.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel