Gwamna Samuel Ortom ya lashe zaben jihar Benuwe karo na biyu

Gwamna Samuel Ortom ya lashe zaben jihar Benuwe karo na biyu

- Gwamna Samuel Ortom ya sake samun nasara a zaben gwamnan jihar Benuwe karo na biyu

- Gwamna Ortom ya lallasa babban abokin hamayyar sa na jam'iyyar APC, Emmanuel Jime

- Ortom ya yi nasara da kimanin kuri'u 434,473 yayin da Jime ya samu kuri'u 342,155

Bayan kai ruwa rana tare aiwatar da bakin gumurzu na siyasa, gwamna Samuel Ortom na jam'iyyar PDP, ya sake lashe zaben gwamnan jihar Benuwe karo na biyu da aka gudanar a ranar Asabar, 23 ga watan Maris, 2019.

Gwamna Samuel Ortom ya lashe zaben jihar Benuwe karo na biyu
Gwamna Samuel Ortom ya lashe zaben jihar Benuwe karo na biyu
Asali: Depositphotos

Gwamna Ortom ya yi nasara da gamayyar kuri'u 434,473, yayin da ya lallasa babban abokin hamayyar sa na jam'iyyar APC, Emmanuel Jime, wanda ya samu kuri'u 345,155 kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito.

Shafin jaridar Legit.ng ya ruwaito cewa, babban Baturen zabe na jihar Benuwe, Farfesa Sabastine Maimako, shi ne ya bayar da wannan sanarwa ta sakamakon zaben a ranar Lahadi, 24, ga watan Maris cikin birnin Makurdi.

KARANTA KUMA: Biyan Albashi: Tsaffin tsagerun Neja Delta sun jinjinawa Buhari

Kazalika cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, shafin jaridar Legit.ng ya ruwaito cewa, gwamna Ortom ya yi karin haske dangane da alakar sa da shugaban kasa Muhammadu Buhari. Ya ce akwai kyakkywar fahimtar juna a tsakani su duk da bambancin akida ta siyasa.

Yayin musanta zargin 'yar rashin ga Miciji tsakanin sa da shugaban kasa Buhari, gwamna Ortom ya yi wannan sanarwa a sansanin dakarun sojin sama da ke birnin Makurdi yayin kirdadon zuwa shugaba Buhari domin yi ma sa lale maraba.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel