Atiku ya taya Gwamna Tambuwal murnar samun nasara

Atiku ya taya Gwamna Tambuwal murnar samun nasara

Atiku Abubakar, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairun da ya gabata, ya taya murna ga zababben gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal.

Gwamna Tambuwal tare da Atiku yayin yakin neman zaben kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a jihar Sakkwato
Gwamna Tambuwal tare da Atiku yayin yakin neman zaben kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a jihar Sakkwato
Asali: Twitter

Tsohon mataimakin shugaban kasa ya mika sakon sa na taya murna ga gwamna Aminu Waziri Tambuwal, a sakamakon samun nasarar lashe zaben cike gurbi na gwamnan jihar Sakkwato da aka gudanar a ranar Asabar, 23 ga watan Maris.

Atiku ya aike da sakon sa na taya murna a shafin sa na sada zumunta jim kadan bayan da hukumar INEC ta shellanta tare da tabbatar da nasarar gwamna Tambuwal a matsayin zababben gwamnan jihar Sakkwato karo na biyu.

KARANTA KUMA: Gwamna Samuel Ortom ya lashe zaben jihar Benuwe karo na biyu

Dan takarar kujerar shugaban kasar ya yabawa al'ummar jihar Sakkwato dangane da yanke wannan kyakkyawan hukunci na sake zaben gwamna Tambuwal domin tabbatar da zaman lafiya, habaka, ci gaba da kuma aminci a fadin jihar.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel