Biyan Albashi: Tsaffin tsagerun Neja Delta sun jinjinawa Buhari

Biyan Albashi: Tsaffin tsagerun Neja Delta sun jinjinawa Buhari

Domin ramawa Kura kyakkyawar aniyyar ta, kungiyar tsaffin tsagerun Neja Delta, ta yi jinjina tare da yabawa alheri da kuma kwazon gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari a sakamakon biyan albashin su na wata akan kari.

Jagoran kungiyar ta tsaffin masu tayar da kayar baya a yankin Neja Delta, Godstime Ogidigba, shi ne ya kwarara wannan yabo ga shugaban kasa Buhari yayin wata sanarwa a ranar Lahadi cikin birnin Benin na jihar Edo.

Farfesa Charles Dokubo
Farfesa Charles Dokubo
Asali: Depositphotos

Mista Ogidigba ya ce kungiyar ta yanke shawarar antaya lambar yabo bisa ga nagartaccen jagoranci na Farfesa Charles Dokubo, babban mai bayar da shawara ta musamman ga shugaban kasa Buhari akan harkokin Neja Delta.

Ya ce kungiyar ta yabawa kwazon gwamnatin shugaban kasa Buhari da kuma Farfesa Dokubo a sakamakon biyan albashin tsaffin tsagerun Neja Delta na kowane wata akan kari da kuma bayar da tallafi na musamman ga Matasan su domin dakile zaman kashe wando.

KARANTA KUMA: Zaben 2019: Kudirin sauya fasalin kasa ya sanya muka juyawa Atiku baya - ACF

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, a yayin da gwamnatin shugaban kasa Buhari ta shimfida shirin afuwa ga tsaffin tsagerun Neja Delta da suka ajiye makamai, kungiyar su a halin yanzu na ci gaba da cin moriya gami da samun alherai na gwamnatin biyo bayan sulhu da ke tsakanin su.

Cikin wani rahoton da shafin jaridar Legit.ng ya ruwaito, a ranar Asabar 23 ga watan Maris, wutar gobara ta lakume wani gida da shaguna daura da hanyar France road da ke unguwar Sabon gari a tantagwaryar birnin jihar Kano.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel