Magudi na Inna-naha kurum aka tafka a Kano – Inji Rabiu Kwankwaso

Magudi na Inna-naha kurum aka tafka a Kano – Inji Rabiu Kwankwaso

Sanata kuma babbban Jagoran jam’iyyyar PDP a jihar Kano, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, yayi kira ga hukumar zabe mai zaman kan-ta watau INEC da ta shirya wani sabon zaben gwamna a Kano.

Sanata Rabiu Kwankwaso ya nemi a soke zaben da aka yi a jihar Kano ne bayan yace an tafka magudi ne kurum bayan an shigo da wasu ‘Yan daba cikin jihar. Kwankwaso ya bayyana wannan ne jiya Asabar 23 ga Watan Maris.

Tsohon gwamnan ya fadawa manema labarai a cikin gidan sa cewa wani babban jami’in tsaro da aka turo zuwa jihar Kano watau DIG Anthony Michael Obizi ya taimakawa masu mulki wajen murde zaben da aka ayi jiya a Jihar.

KU KARANTA: Shugaban PDP yace dole a sake sabon zaben-ciki gibi a Jihar Kano

Magudi na Inna-naha kurum aka tafka a Kano – Inji Rabiu Kwankwaso
Madugun Jam’iyyar PDP na Jihar Kano Kwankwaso yace ba ayi zabe jiya ba
Asali: UGC

Injiniya Rabiu Kwankwaso yake cewa rigingimun da aka tada a wurare da dama na cikin jihar ya sababba magudi a kusan dukkanin mazabun da aka sake zabe. INEC dai ta gudanar da zaben cike-gurbi ne a rumfuna 208 da ke Kano.

Babban ‘dan siyasar ya nuna cewa ‘yan daba sun dangwale kuri’un jama’a tun da sassafe musamman a cikin Kauyukan jihar Kano don haka ya nemi hukumar INEC da tayi watsi da wannan soki-burutsu da aka yi a jihar da sunan zabe.

Kun ji cewa a wasu wurare da-dama a Kano, ‘yan daba ne su ka zagaye harabar zabe inda su ka hana kowa kada kuri’u. Haka kuma an samu ‘yan daba da su ka rike dangwale kaf kuri’un wasu Mazabun.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel