Simon Lalong ya doke Jeramiah Useini a zaben Gwamnan Jihar Filato

Simon Lalong ya doke Jeramiah Useini a zaben Gwamnan Jihar Filato

Gwamnan jihar Filato watau Simon Bako Lalong na jam’iyyar APC ta All Progressives Congress ya lashe zaben gwamna da aka karasa jiya. ‘Dan takarar na APC ya doke jam’iyyar PDP mai adawa.

Simon Lalong wanda yake kan mulki ya samu kuri’a 595, 582 a zaben da aka yi. Babban Abokin takarar sa watau Sanata Jeremiah Useni na PDP kuma ya samu kuri’u 546, 813 ne a zaben da hukumar zabe na INEC ta sanar.

Shugaban jami’ar harkar gona da ke Garin Makurdi, Farfesa Richard Anande Kimber, shi ne ya sanar da sakamakon zaben a madadin hukumar INEC mai zaman kan-ta. Lalong ya smau nasara a kan tsohon Minista kuma Sanatan PDP.

KU KARANTA: ‘Yan bangar siyasa sun hana mutanen Kano kada kuri’ar su

Simon Lalong ya doke Jeramiah Useini a zaben Gwamnan Jihar Filato
Laftana Janar Jeramiah Useini ya sha kashi a zaben Jihar Filato
Asali: UGC

A zaben cike-gurbi da aka yi, jam’iyyar APC da ke mulki ta samu kuri’u 12, 327 daga cikin mazabun da ke kananan hukumomi 9. ‘Dan takarar PDP watau Janar Jeremiah Useni ya tashi ne da kuri’u 8, 487 a karasahen zaben na jiya.

An gudanar da zaben cike-gibi ne a wasu akwatuna 40 na jihar bayan an gaza samun wanda yayi nasara makonni 2 da su ka wuce. Simon Lalong ya samu nasara a irin su, Kanke, Bokkos, Mikang, Pankshin, Kanam da Yankin Jos.

APC ce kuma ta samu nasara a Garuruwan Wase, Mangu, Qua’an Pan, da cikin Shendam inda shi kuma ‘Dan takarar PDP ya kawo Langtang Barkin Ladi, Jos ta Kudu, Riyom, Langtang ta Kudu da kuma karamar hukumar Bassa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel