Kotu ta bayyana yadda INEC ta canja sakamakon zaben gwamna a Osun

Kotu ta bayyana yadda INEC ta canja sakamakon zaben gwamna a Osun

Kotun sauraron korafin zabe ta soki hukumar zabe ta kasa (INEC) bisa rawar da ta taka wajen aikata magudi a zaben gwamnan jihar Osun.

Kotun ta bayyana hakan ne yayin hukuncin da ta yanke a jiya juma'a da ya bayyana dan takarar jam'iyyar PDP, Sanata Ademola Adeleke, a matsayin halastaccen wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Osun da aka yi ranar 28 ga watan Satumba na shekarar 2018.

A hukuncin Jastis Peter Obiorah da Jastis Adegboyega Gbolagunte suka yanke, kotun ta bayyana cewar INEC ce ta canja sakamakon zaben da wakilan jam'iyyu suka saka hannu a kan sa, wanda hakan ya kai ga dan takarar APC, Gboyega Oyetola, ya kai ga nasara.

Sai dai shugaban alkalan kotun, Jastis Muhammad Sirajo, ya ki amincewa da hukuncin da abokansa suka yanke tare da bayyana cewa INEC ba ta nuna son kai ga wani bangare ba.

Kotu ta bayyana yadda INEC ta canja sakamakon zaben gwamna a Osun
Gboyega Oyetola
Asali: UGC

A cikin hukuncin kotun da alakalan kotun biyu suka yanke, sun bayyana cewar tilas su fito fili su yi bayani a kan hujjar da suka dogara da ita wajen bayyana Ademola a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar gwamnan jihar sabanin Oyetola da INEC ta bayyana.

"Hukumar zabe ta canja alkaluman sakamakon zabe da wakilan jam'iyya suka amince da shi. INEC ta canja sakamakon da aka shigar a cikin fom din EC8A bayan wakilan jam'iyya sun saka hannu sun ta fi.

DUBA WANNAN: Yadda INEC tayi min kwangen kuri'u a jihohi 31 - Atiku

"Ya kamata INEC ta sani cewar tana aikin jama'a ne kuma aiki na amana. Kamata ya yi koda yaushe ta kasance mai kokarin kare dokokin zabe," kamar yadda ya ke a cikin hukuncin.

Kotun ta bayyana cewar dogaro da wannan hujja da ta gano ne ya sa ta yanke hukuncin cewar Adegboyega Oyetola na jam'iyyar APC ba shine halastaccen dan takara da jama'ar jihar Osun suka zaba ba. Sakamakon zabe ya nuna cewar Ademola Adeleke ne dan takarar da jama'ar jihar Osun suka zaba a matayin gwamna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel