Babu wani dalilin da zai sa a soke zaben Kano - APC ta yiwa PDP raddi

Babu wani dalilin da zai sa a soke zaben Kano - APC ta yiwa PDP raddi

Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress, APC, Alhaji Abdullahi Abbas, ya bayyana cewa babu wani dalilin da zai sanya a soke zaben gwamnan jihar Kano da ke kan gudana.

Jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party, PDP, ta bukaci soke zaben bisa ga wasu zarge-zargen magudi da take yiwa APC. Amma shugaban APc ya karyata jawabin takwararsa na PDP kan tuhumarsa.

Abbass yace: "Wannan kira da PDP ke yi na soke zaben da ke kan gudana shirme ne. Hukumar INEC ta tabbatar da cewa ta kammala zaben."

"PDP ta jira a sanar da sakamako sannan ta kai kara kotu idan bata amince da sakamakon. Abinda da doka ta tanada kenan. Ina tunanin PDP ta gaza tattara jama'anta."

Shugaban APC ya yi kira ga jami'an tsaro su tabbatar da tsaron rayuka da dukiyan mutane. A kan zargin shigo da mutane da jihar Zamfara, Katsina, Kaduna da Kebbi, Abbass ta karyata rahoton.

KU KARANTA: Shugaban kasa ya sallami manyan hafsoshin tsaro sakamakon kisan soji 23

A bangare guda, Rundunar jami'an tsaron 'yan sanda a jihar Kano ta ce ta kara tura karin jami'an ta a mazabar Gama, karamar hukumar Nasarawa ta jihar Kano sakamakon samun tashe-tashen hankula da aka samu a wasu rumfuna yayin zabukan zagaye na biyu da ake yi.

Jami'in hulda da jama'a na 'yan sandan, DSP Abdullahi Haruna shine ya bayyana hakan a cikin wata fira da yayi da manema labarai ciki hadda majiyar mu ta kamfanin dillancin labaru na Najeriya a garin Kano.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ngLatsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel