Boko Haram: Shugaban kasa ya sallami manyan hafsoshin tsaro sakamakon kisan soji 23

Boko Haram: Shugaban kasa ya sallami manyan hafsoshin tsaro sakamakon kisan soji 23

Shugaban kasar Chadi, Idriss Deby, ya sallami manyan hafososhin sojin kasar bisa da kisan jami'an Soji 23 sakamakon harin Boko Haram.

Deby ya sallami Seid Mahamat da mataimakansa biyu bayan shekaru shida a mulkin da yammacin Juma'a 23 ga watan Maris bayan harin da aka kai kudu maso yammacin kasar.

Da safiyar Juma'a, yan kungiyar Boko Haram sun kaiwa Sojin Chadi mumunan hari a Dangdala inda akalla sojoji 23 suka rasa rayukansu kuma wasu sun jikkata.

Kana ranar Alhamis, yan Boko Haram sun kashe mutane takwas a Karidi, kudu maso gabashin kasar Nijar wanda ke kusa da tafkin Chadi.

KU KARANTA: Rikici ya barke a Kano, an kaiwa yan jarida hari

Dakarun sojin Najeriya, Chadi, Kamaru da NIjar sun hada kai karkashin rundunar sojin kasa da kasa domin kawo karshen rikicin Boko Haram.

A bangare guda, Rundunar soji da ke atisayen LAFIYA DOLE a shiyyar Arewa maso Gabas ta bayyana cewa labarin da ake yadawa na cewar 'yan ta'addan Boko Haram sun mamaye garuruwa hudu a jihar Adamawa karyar banza ce, kuma labari ne da baida tushe.

Shafin jaridar Sahara Reporters ne ya fara wallafa labarin a ranar 4 ga watan Fabreru, wanda rundunar sojin ta kira a matsayin 'karya tsagoronta'.

Mai magana da yawun rundunar, Kanal Onyema Nwachukwu, a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Maiduguri a ranar Talata, ya ce: "Rundunar soji da ke atisayen LAFIYA DOLE ta ci karo da wani rahoto da ake yadawa, wanda ya samo asali daga Sahara Reporters da ta wallafa a shafinta a ranar 4 ga watan Fabreru 2019, cewa Boko Haram ta mamaye garuruwa hudu a jihar Adamawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel