Wayyo Allah: Ana kokarin kassara magoya bayan mu a Bauchi - PDP

Wayyo Allah: Ana kokarin kassara magoya bayan mu a Bauchi - PDP

Babbar jam'iyyar adawa a jihar Bauchi dake shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya ta Peoples Democratic Party (PDP) ta yi kururuwar shelantawa duniya cewa sun samu rahotannin sirri dake tabbatar masu da cewa za'a tayar da husuma sannan kuma a cafke wasu manyan su a jihar.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da jami'in yada labarai na jam'iyyar a mataki na kasa, Mista Kola Ologbondiyan ya fitar ya kuma rabawa manema labarai ranar Asabar.

Wayyo Allah: Ana kokarin kassara magoya bayan mu a Bauchi - PDP
Wayyo Allah: Ana kokarin kassara magoya bayan mu a Bauchi - PDP
Asali: UGC

KU KARANTA: An jefar da jaririya da wasika mai sosa ziciya a Kaduna

A cewar sa, manya-manyan 'yan jam'iyyar ta su ta PDP da aka shirya kamawa sun hada da Alhaji Bello Kirfi, Sanata Abdul Ningi, Sanata Suleiman Nazif, Sanata Isa Hamma Misau, da kuma Alhaji Hamza Akuyam.

Sauran sun hada da shugaban jam'iyyar na PDP a jihar ta Bauchi Hon Salisu Zakari Ningi, Hon Ahmed Yerima, Hon Samaila Burgah da kuma Hon Aminu Tukur.

A wani labarin kuma, Jami'an tsaro a filin sauka da tashin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe na kasa-da-kasa, garin Abuja sun cafke shugaban kamfanin yada labarai na AIT da Ray Power, Mista Raymond Dokpesi yana dawowa daga kasar Dubai inda yake neman lafiya.

Gidan Talabijin din AIT ne dai ya sanar da hakan inda suka ce daya daga cikin jami'an hana shige da fice ta kasa watau yace umurni ne suka samu daga sama na cewa su kama shi da ya dawo Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel