Maimaita zabe: Rundunar 'yan sanda sun tura karin dakaru a mazabar Gaba, jihar Kano

Maimaita zabe: Rundunar 'yan sanda sun tura karin dakaru a mazabar Gaba, jihar Kano

Rundunar jami'an tsaron 'yan sanda a jihar Kano ta ce ta kara tura karin jami'an ta a mazabar Gama, karamar hukumar Nasarawa ta jihar Kano sakamakon samun tashe-tashen hankula da aka samu a wasu rumfuna yayin zabukan zagaye na biyu da ake yi.

Jami'in hulda da jama'a na 'yan sandan, DSP Abdullahi Haruna shine ya bayyana hakan a cikin wata fira da yayi da manema labarai ciki hadda majiyar mu ta kamfanin dillancin labaru na Najeriya a garin Kano.

Maimaita zabe: Rundunar 'yan sanda sun tura karin dakaru a mazabar Gaba, jihar Kano
Maimaita zabe: Rundunar 'yan sanda sun tura karin dakaru a mazabar Gaba, jihar Kano
Asali: Facebook

KU KARANTA: Dan takara ya janye ya koma PDP ranar zabe

DSP Abdullahi ya kara da cewa an tura karin jami'an 'yan sandan ne biyo bayan zagayawar da mataimakin insifectan 'yan sandan, Anthony Micheal a rumfunan mazabar da safiyar yau.

A wani labarin kuma, Hukumar nan ta Najeriya mai zaman kanta dake da alhakin gudanar da zabe a kasar ta mayar wa da kasar Amurka martani akan zarge-zargen da ta yi na cewa zaben da ya gudana ba yi sahihancin da ake tunani can-can ba.

Tun farko dai ofishin jakadancin kasar ta Amurka ya fito da matsayar su ne game da zaben na 2019 da ya gudana a Najeriya in da suka bayyana takaicin su akan yadda suka ce an samu karacin masu kada kuri'u da kuma cinikayyar kuri'a tsakanin 'yan siyasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel