El-Rufai ya bayyana abinda zai yiwa wadanda ba su zabe shi ba

El-Rufai ya bayyana abinda zai yiwa wadanda ba su zabe shi ba

- Gwamnan Jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai ya ce gwamnatinsa ba za ta nuna banbancin wurin yiwa al'umma aiki ba

- Gwamnan ya ce gwamnatinsa za ta yiwa kowa adalci ba tare da la'akari da ko sun zabe shi ko ba su zabe shi ba

- El-Rufai ya ce zabe ya wuce saboda haka yanzu lokaci ne na hada kan al'umma da yin aiki domin cigaban jiha

El-Rufai ya bayyana abinda zai yiwa wadanda suka ki zaben sa
El-Rufai ya bayyana abinda zai yiwa wadanda suka ki zaben sa
Asali: UGC

Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ya dauki alkawarin zai yiwa dukkan al'ummar Kaduna adalci ba tare da la'akari da banbancin siyasa ba.

Gwamnan ya ce zabe ya wuce saboda haka yanzu lokaci ne da ya kamata a fara yiwa al'umma aiki inda ya yi kira ga abokan hammayarsa da magoya bayansa su hada hannu wuri guda domin ciyar da jihar gaba.

DUBA WANNAN: Zaben Gwamna: APC tayi martani a kan nasarar da Adeleke ya yi a kotu

Gwamna El-Rufai ya yi wannan furucin ne a yayin wata liyafar cin abinci da aka shirya domin karrama shi a ranar Juma'a. Ya yi kira ga al'ummar jihar su zauna lafiya da juna kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

"Nayi imanin cewa zabe ya wuce saboda haka yanzu sai mu hadu wuri guda muyi aiki domin kawo hadin kai. Za mu yiwa kowa adalci ba tare da la'akari da cewa mutum ya zabe mu ko bai zabe mu ba. Zabe ya wuce. Yanzu lokacin aiki ne," inji El-Rufai.

A kan tabarbarewar tsaro a wasu garuruwa a jihar, El-Rufai ya ce za a karo jami'an tsaro da za su taimaka wurin kiyaye rayyuka da dukiyoyin wadanda abin ya shafa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel