Ba za a samu rabuwar kai ba wurin fitar da shugaban majalisar dattijai - Lawan

Ba za a samu rabuwar kai ba wurin fitar da shugaban majalisar dattijai - Lawan

Jagora a majalisar dattawa, Sanata Ahmed Lawan mai wakiltar Yobe ta Arewa ya ce batun zaben shugaban majalisar dattawa na majalisa karo na tara ba zai haifar da matsala a jam'iyyar APC ba.

Lawan ya yi wannan tsokacin ne a yayin hira da ya yi da manema labarai a babban birnin tarayya, Abuja kamar yadda Punch ta ruwaito.

Ya ce shugabanin jam'iyyar ta APC sun koyi darasi daga abinda ya faru a yayin zaben shugaban majalisa na majalisar karo ta 8 saboda haka ba za a maimaita kuskuren da ya faru a baya ba.

Bisa ga dukkan alamu jam'iyyar APC ce za ta kasance mai rinjaye a majalisar ta 9 inda ta lashe kujeru 65 cikin 109 a halin yanzu kuma ta samu kujeru 221 cikin 360 na majalisun dokokin tarayya a zaben da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairu.

DUBA WANNAN: Zaben Gwamna: APC tayi martani a kan nasarar da Adeleke ya yi a kotu

Zaben shugaban majalisa ba zai kawo rabuwan kai a APC ba - Lawan
Zaben shugaban majalisa ba zai kawo rabuwan kai a APC ba - Lawan
Asali: Twitter

A watan Yunin 2015, Sanata Bukola Saraki a lokacin yana jam'iyyar APC ne ya zama shugaban majalisar duk da cewa shugabanin jam'iyyar sun fi son Lawan ya zama shugaba.

A majalisar dokokin tarayya nan ma Yakubu Dogara ya yi burus da umurnin jam'iyyar APC inda ya yi takarar shugabancin majalisar ya kuma yi nasara a maimakon Mr Femi Gbajabiamila da jam'iyyar ta fi so ya dare kujerar.

Tare da wasu zababbun sanatoci 10 a wurin taron da aka gudanar a ranar Juma'a, Lawan ya ce, "Bamu tunanin za a samu wata matsala; ba abinda muke fata kenan ba."

"Jam'iyyar mu ta APC ta koyi darasinta saboda haka wannan karon shugabanin jam'iyyar ba za su maimaita kuskuren da akayi a baya ba.

"Na tabbata shugabanin mu za su kula da wannan nasarar da muka samu a APC. Kuma bani shakka jam'iyyar za ta bullo da shirye-shirye da za su dace da irin wadanda gwamnatin Shugaba Buhari keyi," inji Lawan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel