Kwamishinan harkokin musamman na Kano ya fada hannun Jami’an tsaro

Kwamishinan harkokin musamman na Kano ya fada hannun Jami’an tsaro

Jami’an tsaro sun cafke Kwamishinan harkokin musamman na jihar Kano watau Mukhtar Yakassai. Sai dai har yanzu ba mu samu cikakken labari game da abin da ya aukun ba.

Kamar yadda Jaridar Premium Times ta rahoto a yau Asabar 23 ga Watan Maris, ‘Yan Sanda sun damke Mukhtar Yakassai ne bayan ya zo da wasu ‘yan daba inda yayi yunkurin tarwatsa aikin zaben da aka yi a Garin Dala.

Rahoton yace an kama Hon. Mukhtar Yakassai ne a rumfar akwatin da ke cikin Makarantar Sakandaren nan ta Unguwar Yelwa da ke cikin karamar hukumar Dala a Birnin Kano a yayin da jama’a ke shirin kada kuri’ar su.

KU KARANTA: Gwamna Ganduje yana rabawa Ma’aikatan zabe kyautar filaye a Kano

Kakakin ‘Yan Sanda na jihar Kano, Abdullahi Haruna bai iya amsa wayar manema labarai domin ya bada jawabi a game da batun ba. Akwatunan Yelwa da ke Karamar hukumar ta Dala tana cikin wuraren da za a sake zabe.

A wancan karo da aka soma zaben dai, Dakarun ‘Yan Sanda sun damke Kwamishinan harkokin kananan hukumomin jihar Kano watau Murtala Sule Garo a Karamar hukumar Nasarawa yana yunkurin rusa aikin zaben da ake yi.

Dazu kuma mun ji cewa jami’an tsaro sun cafke wani Matashi da yayi kokarin sace kayan zabe. Wannan abu ya faru ne a cikin Unguwar Gama da ke dai cikin Karamar hukumar ta Nasarawa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel