Da zafinsa: Yadda 'yan bangar siyasa suka cinnawa kayan zabe wuta a Benue

Da zafinsa: Yadda 'yan bangar siyasa suka cinnawa kayan zabe wuta a Benue

Rahotannin da muke samu yanzu na nuni da cewa wasu da ake kyautata zaton cewa 'yan ta'adda ne sun bankawa kayan zabe wuta, kayan zaben da aka yi nufin gudanar da zaben gundumar Azendeshi da ke garin Chito, jihar Benue da su.

Chito dai shelkwatar gundumar Azendeshi ce, mai dauke da akalla mutane 13,000.

Rahotanni sun bayyana cewa an ajiye kayayyakin zaben ne a wata makarantar firamare ta gwamnati, kafin wasu 'yan ta'adda da ke aiki karkashin wata jam'iyyar siyasa suka fi karfin jami'an tsaro tare da bankawa kayan zaben wuta.

KARANTA WANNAN: KAI TSAYE: Yadda zaben gwamnan Bauchi zagaye na 2 ke gudana a rumfuna 36

An kuma samu makamancin wannan rahoton a wani yanki na karamar hukumar Kwande, inda wasu 'yan ta'adda suka yi kasa-kasa da wani jami'in INEC tare da lalata kayan zabe, amma dai rahotanni sun bayyana cewa jami'an tsaro sun shawo kan lamarin.

Har zuwa wannan lokaci da aka wallafa wannan labarin, zabe na ci gaba da gudana a wasu rumfunan zabe da ke cikin kananan hukumomi 22 cikin 23 na jihar da ake kan gudanar da zaben gwamnan jihar zagaye na biyu.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel