Da zafinsa: Ana tsakiyar zabe, an yi garkuwa da wasu jami'an INEC guda 4 a Bauchi

Da zafinsa: Ana tsakiyar zabe, an yi garkuwa da wasu jami'an INEC guda 4 a Bauchi

- Wasu 'yan bindiga sun sace wasu jami'an hukumaer zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da ke a jihar Bauchi guda hudu, da har yanzu ba a bayyana sunayensu ba

- Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a karamar hukumar Jama'are, a rumfar zabe ta 02, akwatin zabe mai lamba 010

- Duk wani yunkuri na jin ta bakin hukumar zabe ta jihar Bauchi da kuma rundunar 'yan sanda ta jihar Bauchi ya ci tura

Rahotannin da muke samu yanzu na nuni da cewa wasu 'yan bindiga sun sace wasu jami'an hukumaer zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da ke a jihar Bauchi guda hudu, da har yanzu ba a bayyana sunayensu ba.

Har ya zuwa wannan lokaci da aka kammala rubuta wannan rahoto, lamarin dai na ci gaba da haddasa rudani da tsoro a tsakanin ma'aikatan INEC da kuma al'ummar gari inda har za a iya jiyo hargowar jama'a kan sace jami'an.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a karamar hukumar Jama'are, a rumfar zabe ta 02, akwatin zabe mai lamba 010.

KAI TSAYE: Yadda zaben gwamnan Bauchi zagaye na 2 ke gudana a rumfuna 36

Da zafinsa: Ana tsakiyar zabe, an yi garkuwa da wasu jami'an INEC guda 4 a Bauchi
Da zafinsa: Ana tsakiyar zabe, an yi garkuwa da wasu jami'an INEC guda 4 a Bauchi
Asali: Twitter

Wani ma'aikacin INEC, wanda ya tsallake rijiya ta baya baya ya ce 'yan bindigar sun zo ne cikin motoci kirar Toyota Hilux guda bakwai.

A cewarsa, an sace jami'an zaben ne tare da kayayyakin zabe.

Duk wani yunkuri na jin ta bakin shugaban sashen ilimantar da masu kad'a kuri'a da hulda da jama'a na ofishin INEC da ke Bauchi, Ahmed Waziri ya ci tura.

Duk wani yunkuri na jin ta bakin mai magana da yawun rundunar 'yan sanda ta jihar Bauchi, Kamal Datti Abubakar ya ci tura.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel