Sayen kuri'u: Wakilan jam'iyya suna cin karensu babu babbaka a Sokoto

Sayen kuri'u: Wakilan jam'iyya suna cin karensu babu babbaka a Sokoto

Duk da jami'an tsaro masu yawa da suka hada da 'yan sanda, DSS, NSCDC, Mobile Police a Jami'an Hukumar Kiyaye Haddura, FRSC da aka girke a rumfunan zabe a kananan hukumomin Kware, Gwadabawa da Illela, hakan bai hana cinikin kuri'a ba.

Daily Trust ta ruwaito cewa baya ga sayan kuri'un, an kuma gano wakilan jam'iyyun suna karbar takardan kuri'a daga hannun masu zabe suna dangwale musu sannan su jefa cikin akwatin zabe.

An rumfar zabe na gidan Katta da ke Illela a jihar Sokoto, wakilan jam'iyya sun ci karensu babu babbaka inda aka gansu suna ciniki da masu zabe kuma daga baya suka rika karbar takardun kuri'arsu suna dangwalawa a madadin su.

DUBA WANNAN: Zaben Gwamna: APC tayi martani a kan nasarar da Adeleke ya yi a kotu

Sayen kuri'u: Wakilan jam'iyya suna cin karensu babu babbaka a Sokoto
Sayen kuri'u: Wakilan jam'iyya suna cin karensu babu babbaka a Sokoto
Asali: Twitter

Daga bisani, wakilan jam'iyyun sun fara rikici tsakaninsu a kan zargin cewa wasu na yin babakere a kan kuri'un masu zabe.

Daya daga cikin wakilan jam'iyyun, mai suna Aminu da ya ce shi dan Illela ne ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa sun yiwa jami'an INEC da jami'an tsaro korafi a kan lamarin amma sai suka fada musu bai aikinsu bane.

Cikin fushi, daya daga cikin magoya bayan jam'iyya, Rabiu Ilela ya yi Allah wadai da cinikin kuri'un inda ya daga murya yana cewa, "Mun san su, mun san daga inda suka fito da wadanda suka turo su. Ba mu son rigima shi yasa mu kayi shiru muna jira mu ga abinda zai faru."

Wakilan jam'iyyu suna tsaye kusa da jami'an INEC na wucin gadi yayin da ake cinikin kuri'un kuma jami'an tsaro suna kallo.

Wani jami'in tsaro a rumfar zaben ya shaidawa wakilin Daily Trust cewa babu abinda zai iya yi saboda saura jami'an tsaron ba su ce komi ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel