Jam’iyyar PDP tace dole a sake sabon zaben-ciki gibi a Jihar Kano

Jam’iyyar PDP tace dole a sake sabon zaben-ciki gibi a Jihar Kano

Shugaban jam’iyyar PDP mai adawa a jihar Kano, Dr. Rabiu Suleiman Bichi ya nemi ayi maza a soke zaben cike-gibi da aka gabatar a cikin kananan hukumomi kusan 30 da aka shirya a fadin jihar Kano.

Rabiu Suleiman Bichi yace sam ba zabe aka yi a jihar Kano ba. Shugaban jam’iyyar adawar na rikon kwarya ya bayyana cewa APC tayi hayar ‘yan daba ne daga Garuruwa irin su Zamfara, Katsina, Kaduna da kuma Filato.

Dr. Rabi’u Bichi a wata zantawa da yayi da manema labarai dazu ya bayyana cewa an baza wadannan ‘yan iskan gari da aka kawo cikin Garin Kano a kowace rumfar zabe da aka shirya za a gudanar da zaben cike-gibi a jihar.

KU KARANTA: Zaben cike-gibi ya sa ‘Yan Kwankwasiyya sun ajiye jar hula

Jam’iyyar PDP tace dole a sake sabon zaben-ciki gibi a Jihar Kano
Jam'iyyar PDP ta ce a soke zaben Gwamnan Jihar Kano
Asali: Twitter

Jam’iyyar adawar ta koka game da yadda wadannan ‘yan daba su ka rika yawo da makamai dauke da katin zaben wasu mutane ba tare da an taka masu burki ba. Rabiu Bichi yace wasu ‘yan daban sun yi shiga ne kamar jami’an INEC.

Mukaddashin shugaban na PDP ya kuma kara da cewa an kona motocin Magoyan su, sannan kuma har ta kai an kashe Wakilan da PDP ta aika zuwa Yankunan Doguwa, Nasarawa, Minjibir, Dala da kuma Tudun Wada a zaben na yau.

A karshe Rabiu Bichi yayi kira ga hukumar zabe mai zaman kan-ta watau INEC ta soke daukacin zaben na cike-gibi da aka yi domin a cewar sa, PDP ta cire rai da cewa za ayi adalcin da ya dace a zaben.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel