Zaben Kano: An fatattaki masu shirin kada kuri’a a Gama

Zaben Kano: An fatattaki masu shirin kada kuri’a a Gama

Labari ya zo mana daga gidan jaridar BBC Hausa cewa an tarwatsa wadanda ke kan layin zabe a rumfar Mai garin Gama. Mazabar Gama ta na cikin inda ake sake zaben gwamna yau a jihar Kano.

Zaben Kano: An fatattaki masu shirin kada kuri’a a Gama
An tarwatsa layin zabe a rumfar Mai garin Gama
Asali: Facebook

BBC Hausa sun rahoto cewa wasu ‘yan iskan gari sun shigo cikin Gama a daidai lokacin da jama’a su ke kan layin zabe da nufin kada kuri’ar su. Nan take dai su ka kori jama’a daga rumfunan zaben da ke gaban gidan Mai Garin.

Kamar yadda labarin ya zo mana, wannan ya sa mutane su ka tsere daga akwatin da ke gaban Lawalin wannan yanki. Manema labarai sun tabbatar da cewa makamai ne kurum ke yawo a wuraren da ake shirin zaben cike gibin.

KU KARANTA: Gwamna Ganduje yana rabawa Ma’aikatan zabe kyautar filayen Kano

Dazu dai mun ji cewa wasu ‘yan iskan gari sun yi fata-fata da motar ‘dan jaridar NTA bayan an kuma hana menama labarai na gidan Talabijin na TVC daukan rahoto a cikin Garin Gama da ke cikin karamar hukumar Nasarawa.

Yanzu dai mun fara samun rade-radin cewa jami’an tsaro na jihar Kano sun yi maza sun kai dauki zuwa cikin wannan Gari na Gama inda ake sa rai mutum 40, 000 za su kada kuri’ar su a zaben yau.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel