Da duminsa: INEC ta soke gudanar da zabe zagaye na biyu a wata mazaba a Bayelsa

Da duminsa: INEC ta soke gudanar da zabe zagaye na biyu a wata mazaba a Bayelsa

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta dakatar da ci gaba da gudanar da zabe zagaye na biyu na mazabar Brass da ke jihar Bayelsa biyo bayan wani umurni da babbar kotun gwamnatin tarayya da ke da zama a Yenagoa ta bata na dakatar da zaben.

Kwamishinan hukumar INEC na jihar, Pastor Monday Udo Tom a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Yenagoa a ranar Asabar, ya ce INEC a matsayinta na mai bin doka da oda, ta bi wannan umurni da kotu ta bata na dakatar da zaben mazabar.

Sai dai, Tom ya bayyana cewa zaben zagaye na biyu zai gudana a mazabu biyu na gundumar Ogbia II da kuma kudancin Ijaw IV inda aka bayyana zabensu a matsayin zaben da bai kammala ba a ranar 9 ga watan Maris, 2019.

KARANTA WANNAN: Tabbas kaine ka ci zabe a Kaduna, amma a mafarkinka - El-Rufai ya zolayi Atiku

Da duminsa: INEC ta soke gudanar da zabe zagaye na biyu a wata mazaba a Bayelsa
Da duminsa: INEC ta soke gudanar da zabe zagaye na biyu a wata mazaba a Bayelsa
Asali: Getty Images

Ya ce: "Mun dakatar da ci gaba da gudanar da zabe zagaye na biyu a mazabar Brass 1, gunduma ta 6, rumfar zabe ta 11-16, biyo bayan wani umurni da babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Yenagoa ta aiko mana mai dauke da lamba FHC/YNG/C5/41/2019 da kwanan wata 22 ga watan Maris, 2019.

"A matsayinmu na masu bin dokokin kasar nan, hukumar za ta sanar da masu ruwa da tsaki da zaran umurnin kotun ya lalata kan dakatar da zaben mazabar Brass ta I," a cewar sanarwar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel