Gwamna Lalong ya yi murna ta samun nasarar tazarce

Gwamna Lalong ya yi murna ta samun nasarar tazarce

Gwamnan jihar Filato, Simon Balo Lalong, bayan samun nasarar tazarce akan kujerar sa ta gwamnati yayin zaben cike gurbi da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata, ya yi furuci na bayyana farin ciki da mika godiya.

Gwamna Simon Lalong
Gwamna Simon Lalong
Asali: UGC

Biyo bayan nasarar sa a zaben gwamnan jihar Filato da aka kammala a ranar Asabar, Gwamna jihar Filato na neman goyon bayan dukkanin al'ummar jihar sa da kuma masu ruwan tsaki domin samun dama ta tabbatar da kwararar romon dimokuradiyya.

Gwamnan yayin da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta watau INEC ta tabbatar da nasarar sa cikin birnin Jos a ranar Lahadi, 24 ga watan Maris, ya yi kira na neman goyon bayan al'ummar jihar Filato da kuma dukkanin masu ruwa da tsaki a fannin siyasa domin cimma manufa ta samun nasara da ci gaba a gwamnatin sa cikin wa'adin ta na biyu.

Bayan bayyana farin cikin da mika sakon jinjina gami da godiya ga al'umma da suka sake danka ma sa akalar jagoranci a karo na biyu, Gwamna Lalong ya ce akwai muhimmancin hadin da kuma tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali domin fidda jihar Filato zuwa tudun tsira.

KARANTA KUMA: Zaben cike gurbi: Gwamna Ganduje ya samu rinjayen nasara a kananan hukumomi 8 na jihar Kano

Lalong ya kuma yabawa kwazon hukumar INEC, jami'an tsaro, manema labarai da masu kuri'a a sakamakon yadda zaben ya wakana cikin annashuwa ta mafi kololuwar zaman lafiya da kwanciyar hankali. Ya ce zaben jihar Filato ya kasance mafi lumana yayin gudanar sa.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, gwamna Lalong ya samu nasara da kimanin kuri'u 595,582 inda ya lallasa babban abokin adawar sa na jam'iyyar PDP, Janar Jerimiah Husseini, wanda ya samu kuri'u 546,813.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel