Zaben cike gurbi: Gwamna Ganduje ya samu rinjayen nasara a kananan hukumomi 8 na jihar Kano

Zaben cike gurbi: Gwamna Ganduje ya samu rinjayen nasara a kananan hukumomi 8 na jihar Kano

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, na ci gaba sa samun rinjayen nasara fiye da babban abokin adawar sa na jam'iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf yayin zaben cike gurbi na gwamnan jihar da aka gudanar a ranar Asabar, 23 ga watan Maris.

Yayin hukumar zabe ta bayyana sakamakon zaben kananan hukumomi 8 cikin 28, Gwamna Ganduje ya samu rinjayen nasara da kimanin kuri'u 6,473 yayin da Abba Yusuf ya samu kuri'u 970 kacal.

Zaben cike gurbi: Gwamna Ganduje ya samu rinjayen nasara a kananan hukumomi 8 na jihar Kano
Zaben cike gurbi: Gwamna Ganduje ya samu rinjayen nasara a kananan hukumomi 8 na jihar Kano
Asali: UGC

A zaben gwamnan jihar Kano da aka gudanar a ranar 9 ga watan Maris wanda hukumar INEC ta kaddamar da cewa bai kammala ba, Abba Yusuf na jam'iyyar PDP ya lashe kuri'u 1,014,474 yayin da Gwamna Ganduje na jam'iyyar APC ya samu kuri'u 987,819.

Sai dai yayin da ake ci gaba da tattara sakamakon zaben cike girbi, wakilan jam'iyyar PDP sun nuna rashin goyon baya dangane da yadda zaben ya gudana a fadin jihar Kano tare da cewar cike ya ke da ababe masu cin karo da tanadi na dimokuradiyya.

Wakilan PDP sun yi kira na neman ko akwai wani tanadi na daban da ake yiwa wasu jam'iyyun duba da yadda rikici gami da tarzoma su ka sanya hukumar INEC ta soke zaben wasu yankunan Kano yayin zaben da ya gabata makonni uku da suka shude.

KARANTA KUMA: 2019: Na bayar da gagarumar gudunmuwa a zaben bana - Tinubu

Kazalika a can birnin Shehu kuma, hukumar zabe ta bayyana sakamakon zaben cike gurbi na kananan hukumomi 9 inda jam'iyyar adawa ta PDP ke ci gaba da samun rinjayen nasara fiye da na jam'iyyar APC.

Yayin zaben asali da aka gudanar a ranar 9 ga watan Maris, gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal na jam'iyyar PDP, ya samu rinjayen nasara da kimanin kuri'u 489,558 yayin da na jam'iyyar APC, Alhaji Ahmed Aliyu, ya lashe kuri'u 486,145.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel