PDP ta nemi INEC ta sanar da nasarar Abba Yusuf a jihar Kano

PDP ta nemi INEC ta sanar da nasarar Abba Yusuf a jihar Kano

Jam'iyyar PDP ta yi kira na neman hukumar zabe ta kasa INEC, akan ta yi gaggawar sanar da dan takarar ta, Abba Kabir Yusuf, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kano.

PDP ta yi wannan kira bisa ga madogara ta cewar dan takarar ta shi ne ya lashe zaben da kaso biyu bisa uku na kuri'un da aka kada yayin zaben.

Jam'iyyar ta ce ba bu wani ingataccen zabe na gaskiya da ya wakana yayin zaben cike gurbi da hukumar INEC ta gudanar a ranar 23 ga watan Maris da cewar ba bu wani kage da za ta aminta da shi wajen kwace nasarar dan takarar ta da a halin yanzu yake da rinjaye na fiye da kuri'u 26,000.

PDP ta nemi INEC ta sanar da nasarar Abba Yusuf a jihar Kano
PDP ta nemi INEC ta sanar da nasarar Abba Yusuf a jihar Kano
Asali: UGC

Kamar yadda shafin jaridar Vanguard ya ruwaito, hukumar INEC na da kyakkyawar masaniya ta yadda ‘yan ta'ada da masu tayar da zaune tsaye suka gurbata zaben cike gurbi da aka gudanar a jihar Kano ta hanyar haramtawa al'umma kada kuri'u daidai da ra'ayoyi da kuma tanadi na ‘yancin su da kundin tsarin mulki ya gindaya.

PDP ta ce hukumar zabe ba za ta karbi sakamakon zaben ba sakamakon yadda jam'iyyar APC ta ci Karen ta ba bu babbaka domin yunkurin rinjayar da nasara a gare ta.

KARANTA KUMA: 2019: Na bayar da gagarumar gudunmuwa a zaben bana - Tinubu

Yayin bayyana fushin ta biyo bayan ababe na dakile kwararar romon dimokuradiyya, PDP ta ce tuni al'ummar jihar Kano su ka karkatar da ra'ayin su wajen zaben Abba Yusuf a matsayin jagora yayin zaben gwamnan jihar Kano da aka gudanar a ranar 9 ga watan Maris.

Babbar jam'iyyar ta adawa ta yi kira ga hukumar INEC akan aiwatar da abinda ya dace ta hanyar sanar da Abba Yusuf a matsayin zababben gwamnan jihar Kano biyo bayan tabbatar da duk wata bukata ta sashe na 179 sakin layi na 2 cikin kundin tsarin mulkin kasar nan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel