An cafke ma'aikatan INEC 4 a jihar Bauchi

An cafke ma'aikatan INEC 4 a jihar Bauchi

Da sanadin shafin jaridar The Cable mun samu rahoton cewa, jami'an tsaro rike da makamai sun yi awon gaba da wasu ma'aikata hudu na hukumar zabe ta INEC a jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.

Majiyar rahoton ta bayyana cewa, mummunan al'amarin ya auku a mazaba ta biyu cikin rumfar zabe ta 10 a karamar hukumar Jama'are da ke jihar Bauchi.

An yi awon gaba da ma'aikatan INEC 4 a jihar Bauchi
An yi awon gaba da ma'aikatan INEC 4 a jihar Bauchi
Asali: Twitter

Daya cikin ma'aikatan INEC da ya tsallake wannan hari ya bayyana cewa, jami'an tsato rike da ya miyagun makamai sun yi awon gaba da abokanan aikin sa cikin wasu motoci bakwai kirar Toyota Hilux.

Jami'in na hukumar INEC da ya tsallake rijiya da baya ya bayyana cewa, jami'an tsaron sun yashe ma'aikatan na INEC tare da kayayyakin su na aikin zabe.

Rahotanni sun bayyana cewa, a ranar Asabar, 23 ga watan Maris aka gudanar da zaben cike gurbi cikin jihar Bauchi da wasu jihohi musamman a Arewacin Najeriya.

KARANTA KUMA: 2019: Na bayar da gagarumar gudunmuwa a zaben bana - Tinubu

Mun samu cewa manema labarai sun yi gudun neman tsira yayin da ‘yan ta'ada suka haramta ma su neman abinci yayin zaben cike gurbi a mazabar Gama da ke karamar hukumar Nasarawa a jihar Kano.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, ‘yan ta'adda rika da makamai sun fatattaki ‘yan jarida da masu kada kuri'u a wasu mazabu na jihar Kano

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel