2019: Na bayar da gagarumar gudunmuwa a zaben bana - Tinubu

2019: Na bayar da gagarumar gudunmuwa a zaben bana - Tinubu

Tsohon gwamnan jihar Legas kuma Kanwa Uwar gamin jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya ce ya taka muhimmiyar rawa ta gani da tayi tasirin gaske yayin babban zaben kasa a bana.

Jigon na APC ya ce sauran ababe da suka yi tasiri a zaben bana sun hadar da kwarewar sa a fannin siyasa da kuma jajircewar sa wajen aiwatar da yakin zabe cikin salo da hadin kan magoya baya.

Buhari da Tinubu
Buhari da Tinubu
Asali: Facebook

Tinubu ya bayyana hakan a ranar Juma'a yayin martani kan zargin sa da kulla kutungwila da shugaban hukumar zabe ta INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu, domin rinjayar da sakamakon zaben cike gurbi na gwamnan jihar Sakkwato.

Tsohon gwamnan ya gargadi kungiyar magoya bayan jam'iyyar PDP reshen jihar Sakkwato bisa jagorancin shugabanta, Injiniya Haruna Usman Shagari, da ta dawo daga rakiyar wannan mummunan zargi maras hujja.

KARANTA KUMA: INEC ta fidda sunayen jihohi 18 da za ta gudanar da zaben cike gurbi a ranar Asabar

Tinubu ya ce wannan zargi ba ya da wani tushe ko madogara ta gaskiya da ake yi akan sa da kuma shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, Sanata Adamu Aliero da kuma gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari.

A karshe Tinubu ya nemi jam'iyyar PDP reshen jihar Sakkwato da ta kauracewa bata ma sa suna da shafa ma sa baki fyanti domin cimma wata manufa ta soyuwar zukatan sa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel