Ka daina amfani da sunana kana damfarar jama'ar Sokoto - Tinubu ya gargadi Tambuwal

Ka daina amfani da sunana kana damfarar jama'ar Sokoto - Tinubu ya gargadi Tambuwal

- Bola Tinubu, ya gargadi Aminu Waziri Tambuwal da ya kauracewa amfani da sunansa wajen damfarar al'ummar jihar Sokoto

- Ya yi wannan gargadi a matsayin martani ga wata sanarwa da aka fitar wacce ke zarginsa da murde zaben jihar Sokoto

- Da ya ke nuni da cewa Tambuwal na borin kunya ne kawai ganin faduwa karara a gabansa, ya ce gwamnan na tsoron cewa karshen siyasarsa ce ta zo

Bola Tinubu, ja-gaban jam'iyyar APC na kasa, ya gargadi Aminu Waziri Tambuwal, gwamnan jihar Sokoto, da ke neman tazarce karkashin jam'iyyar PDP, da ya kauracewa amfani da sunansa wajen damfarar al'ummar jihar Sokoto.

Ya yi wannan gargadi a matsayin martani ga wata sanarwa da aka fitar wacce ke zarginsa da murde zaben jihar Sokoto.

Ya bayyana wannan matsayar ta sa a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Juma'a a Legas, a yayin da ya ke kuma yin martani kan zargin da ake yi masa na cewa ya gana da shugaban hukumar zaben kasa INEC domin murde zaben gwamnan jihar Sokoto da za a gudanar zagaye na biyu da nufin baiwa APC nasarar zaben.

KARANTA WANNAN: Tabbas kaine ka ci zabe a Kaduna, amma a mafarkinka - El-Rufai ya zolayi Atiku

Tambuwal
Tambuwal
Asali: UGC

Da ya ke misalta Tambuwal a matsayin "mutumin da ya dulmiye", ya kalubalanci gwamnan da yi amfani da duk wasu hanyoyi domin ganin ya lashe zabe a jihar, kamar yadda kamfanin dillacin labarai na kasa NAN ya ruwaito.

Da ya ke nuni da cewa Tambuwal na borin kunya ne kawai ganin faduwa karara a gabansa, ya ce gwamnan na tsoron cewa karshen siyasarsa ce ta zo, yana mai cewa, "idan har ya rasa wannan zaben, to kuwa ya rasa komai na sa."

Sanarwar ta kuma gargadi Tambuwal da ya ji da matsalolin da ke fuskantarsa a halin yanzu, ya fita daga sha'anin Tinubu da kulla masa sharri ko yi masa kazafi, kasancewar Tinubu mutum ne da ke da'awar samar da nagartacciyar demokaradiyya a kasar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel