Yanzu-yanzu: Rikici ya barke a Kano, an kaiwa yan jarida hari

Yanzu-yanzu: Rikici ya barke a Kano, an kaiwa yan jarida hari

Wasu yan jarida masu daukan cikamakin zaben gwamna a jihar Kano ranan Asabar sun tsallake rijiya da baya yayinda wasu yan baranda dake makarantar Firamaren Suntulma da ke Gama, karamar hukumar Nasarawa suka kai musu hari.

NAN ta bada rahoton cewa yan daban sun fitittiki yan jaridan da ke daukan hotuna a rumfar zaben.

Rikicin ya fara ne lokacin da manema labarai suka kokarin hira da mutanen da aka hana shiga rumfar zaben da ke Makarantar.

Yayinda yan jaridan ke kokarin arcewa, daya daga cikinsu ya fadi. Sai ya shige wani masallaci domin ceton rayuwarsa.

Yan jaridan da aka kaiwa hari sune Maduabuchi Nmeribe na jaridar The Authority, da Kola Oyelere na jaridar Tribune.

Wasu mazauna Gama sun bayyanawa manema labarai cewa an hanasu kada kuri'arsu kuma an fitittikesu daga wajen.

Daya daga cikinsu, Aminu Tijjani, ya laburta cewa yayinda ya tafi makarantar Firamaren domin kada kuri'arsa, dole ya gudu saboda harin yan daba.

Tijjani yace: "Abun babu kyau gaba daya kuma ba haka ake gudanar da zabe ba inda aka hana jama'a kada kuri'arsu."

Wani mazaunin Sani abdullahi, yace ya zo zabe tun misalin karfe 8 amma wasu yan daba sun koresa.

KU KARANTA: Yadda zagayen zabe na biyu ke gudana a jihar Benue

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel