Siyasar Kano: Zaben Gwamna ya zama rikici tsakanin ‘Yan daba a wuraren da ake sake zabe

Siyasar Kano: Zaben Gwamna ya zama rikici tsakanin ‘Yan daba a wuraren da ake sake zabe

Jaridar nan ta Daily Trust ta rahoto cewa rigingimu sun kaure yayin da ake kokarin zaben gwamna a jihar Kano. A yau ne da hukumar INEC mai zaman kan-ta, ta shirya gudanar da zaben cike-gibi a wasu bangarori na jihar Kano.

‘Yan jarida sun tabbatar da cewa zai yi matukar wahala a iya yin zabe a jihar Kano a sakamakon ‘yan daba da aka shigo da su ko ta ina wanda su ke fatattakar jama’a daga filin kada kuri’a inda ake fama da karancin jami’an tsaro.

Kamar yadda Jaridar ta rahoto, an karyawa wani Bawan Allah hakora bayan yayi yunkurin kada kuri’ar sa a Unguwar Masaka da cikin karamar hukumar Dala a Birni. Jami’an ‘yan sanda dai sun gaza yin komai a wadannan yanki.

KU KARANTA: Zaben cike-gibi ya sa ‘Yan Kwankwasiyya sun ajiye jar hula

A cikin Garin na Dala inda za a sake zabe a wasu mazabu, Wakilan jam’iyyar APC kuru make hange inda ake zargin cewa an fatattaki ‘yan adawa. Babu abin da ake kuma gani sai tarin makamai daga magoya bayan ‘yan siyasa.

Manema labarai sun bada tabbacin cewa ‘yan daba sun zagaye cikin Birni da Kauyuka a duk yankunan da ake karasa zaben a yau. A cikin Unguwar Gwammaja ma dai an shigo da ‘yan daba da su ka hana mutane yin zabe.

Dazu dai mun ji cewa wasu ‘yan iskan gari sun yi fata-fata da motar ‘dan jaridar NTA bayan an kuma hana menama labarai daukan rahoto a cikin Garin Gama da ke cikin karamar hukumar Nasarawa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel