Da duminsa: Sa'o'i kadan kafin zabe, Dan takarar APC a Ebonyi ya koma PDP

Da duminsa: Sa'o'i kadan kafin zabe, Dan takarar APC a Ebonyi ya koma PDP

Nome Innocent, Dan takarar kujerar majlisar jihar a karkashin jam'iyyar All Progressive Congress (APC) in Ebonyi State has decamped to the Peoples Democratic Party (PDP) kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito.

Ana sa ran za a gudanar da zabukan ciki gibi ne a mazabu uku a jihar ta Ebonyi.

Kamfanin dillancin labarai NAN ta ruwaito cewa dan takarar na APC a mazabar Ezza ta Arewa ya goyi bayan dan takarar jam'iyyar PDP, Friday Nwuhuo bayan ya fice daga APC.

Ya sanar da ficewarsa ne a wurin taron manema labarai da ya kira a Abakaliki inda Nome ya ce ya dauki matakin ficewa daga APC ne saboda ya lura jam'iyyar ba ta bayar da himma game da zaben.

DUBA WANNAN: Sule Lamido ya fadi yadda APC da Kwamishinan 'yan sanda suka yiwa PDP magudin zabe

Da duminsa: Sa'o'i kadan kafin zabe, Dan takarar APC a Ebonyi ya koma PDP
Da duminsa: Sa'o'i kadan kafin zabe, Dan takarar APC a Ebonyi ya koma PDP
Asali: Twitter

Ga wani sashi daga cikin sanarwar da ya fitar: "Babban matsalar dai itace rashin jajircewa na jam'iyyar APC a jihar mu inda har ta kai ga dan takarar gwamna ya rasa kawo akwatinsa a zaben shugaban kasa da 'yan majalisun tarayya.

"Hakan na nuna cewa APC ba ta shiryawa zaben ba hakan na nufin bata lokacin mu kawai za muyi.

"Bayan tattaunawa da iyalai na da 'yan uwan na 'yan siyasa, na yanke hukuncin murabus daga APC kuma na janye daga zaben cike gibi da za a gudanar ranar Asabar 23 ga watan Maris a mazabar Ezza ta Arewa.

"Babu wanda ya tilasta min daukan wannan matakin sai dai kawai domin ina son in hada kai da zabbaben Gwamna, Injiniya David Umahi domin cigaban Jihar Ebonyi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel