Tabbas kaine ka ci zabe a Kaduna, amma a mafarkinka - El-Rufai ya zolayi Atiku

Tabbas kaine ka ci zabe a Kaduna, amma a mafarkinka - El-Rufai ya zolayi Atiku

- Nasir El-Rufai ya mayar da martani akan wani ikirari da Atiku Abubakar ya yi, na cewar shi ne ya lashe zabe a jihar Kaduna

- A cewar gwamnan, Atiku ya ci zaben jihar Kadunan ne a cikin mafarkinsa kuma zai rasa Kaduna fiye da sau 10 ko da nan gaba

- Ya yi zargin cewa karin kuri'u 100,000 da Atiku ya samu an yi aringizonsu ne kasancewar ba ayi amfani da na'urar 'Card Reader' a wasu sassa na jihar ba

Nasir El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna, ya mayar da martani akan wani ikirari da Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP ya yi, na cewar shi ne ya lashe zabe a jihar Kaduna, a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 23 ga wata Fabreru.

A cewar gwamnan, Atiku ya ci zabe a jihar Kaduna "amma a cikin mafarkinsa" kuma "zai rasa Kaduna fiye da sau 10, saboda dama can bai taba cin jihar Kaduna a wani zaben shugaban kasa ba".

Ya bayyana hakan a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai na fadar shugaban kasa a ranar Juma'a, bayan wata ziyara da ya kaiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kaksar da ke Abuja.

KAI TSAYE: Yadda zaben gwamnan Bauchi zagaye na 2 ke gudana a rumfuna 36

Tabbas kaine ka ci zabe a Kaduna, amma a mafarkinka - El-Rufai ya zolayi Atiku
Tabbas kaine ka ci zabe a Kaduna, amma a mafarkinka - El-Rufai ya zolayi Atiku
Asali: Facebook

Ya ce: "Nima na ji wannan batun. Alal haki, na yi tunanin ko dai da wasa ya ke yi amma da na bincika sai na ga cewa tabbas shi fa da gaske ya ke yi na cewar shine ya lashe zabe a Kaduna. To inaga sai dai idan a mafarkinsa ne a ci zabe a jihar tawa.

"Bari na sanar da ku wannan ba tare da fargabar fuskantar kalubale a nan gaba ba, tunda shugaban kasa Buhari ya fara tsayawa takarar shugabancin kasar a 2003, bai taba shan kaye a jihar Kaduna ba. Don haka, PDP ba ta taba cin zabe a Kaduna ba tun 2003, duk da kuwa su ke da gwamnatin jihar a hannunsu tun daga 2003 har zuwa 2015, ba su taba cin zabe a jihar ba.

"Ya fadi warwas a Kaduna; duk da cewa kuri'u 100,000 da ya yi ikirarin ya samu an yi aringizonsu ne kasancewar an yi zaben wasu sassa na jihar ba tare da yin amfani da na'urar 'Card Reader' ba. Ta wannan dalilin ne har ya samu kuri'u 400,000."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel