Zaben Kano: An fara sakin sakamakon zaben cike-gurbi na Gwamna
Yanzu haka rahotanni na zuwa mana cewa an fara fitar da sakamakon zaben cike-gurbi da aka gudanar a jihar Kano dazu inda aka yi ta samun rikici a wasu mazabun da ake karasa zaben yau a cikin jihar.
Sakamakon da aka fitar ya nuna cewa Abdullahi Umar Ganduje na jam'iyyar APC ne ke kan gaba a zaben inda yake lallasa 'Dan takarar PDP Abba Kabiru Yusuf a mafi yawan kananan hukumomin da aka bayyana sakamakon zaben.
Sakamakon
APC - 45,876
PDP - 10,239
Sababbin sakamakon zabe su na cigaba da fitowa daga Kano:
Karamar hukumar Nasarawa
APC 10,536
PDP 3,409
Karamar hukumar Kibiya
APC 371
PDP 228
Karamar hukumar Dala
APC 2905
PDP 3138
Karamar hukumar Tudun wada
APC 2557
PDP 508
Karamar hukumar Doguwa
APC 1998
PDP 24
Karamar hukumar Albasu
APC 1804
PDP 66
KU KARANTA: Jigon PDP Sanata Kwankwaso ya nemi a sake zabe a Jihar Kano
Karamar hukumar Tofa
APC 628
PDP 190
Karamar hukumar Gaya
APC 1051
PDP 526
Karamar hukumar Bichi
APC: 1,969, PDP: 39
Karamar hukumar Bebeji
APC: 205, PDP: 0;
Karamar hukumar Rogo
APC: 1,033, PDP: 162;
Karamar hukumar Karaye
APC: 1,317, PDP: 27;
Karamar hukumar Rimin Gado
APC: 1,463, PDP: 12;
Karamar hukumar Warawa
APC: 501, PDP: 152
Karamar hukumar Rano
APC: 2,337, PDP: 37;
KU KARANTA: An sake yin ram da wani Kwamishinan Jihar Kano a Ranar zabe
Sauran sakamakon da aka fitar sun hada da:
Karamar hukumar Dambatta
APC: 608, PDP:24;
Karamar hukumar Takai
APC: 4,221, PDP: 149;
Karamar hukumar Albasu
APC: 1,804, PDP: 66;
Karamar hukumar Gabasawa
APC: 728, PDP: 329;
Karamar hukumar Minjibir
APC: 2,414, PDP: 226;
A baya an fitar da sakamakon irin su:
Karamar hukumar Garun Malam
APC - 235
PDP - 01
Karamar hukumar Gezawa
APC= 167
PDP= 27
Karamar hukumar Madobi
APC= 908
PDP= 164
Dawakin Kudu LGA
APC 248
PDP 62
Karamar Hukumar Kibiya
APC - 984
PDP - 05
KU KARANTA: ‘Yan bangar siyasa sun hana mutanen Gama kada kuri’ar su a Kano
Sai dai rahotanni daga Jaridar BBC Hausa sun bayyana cewa an fattataki Ma’aikatan yada labarai na TVC daga cikin Garin Gama inda ake sa rai mutanen kusan 40, 000 za su kada kuri’ar su.
Masu lura da zabe daga wata kungiyar Cleen Foundation sun kuma bayyana cewa babu zaben da yake gudana a irin su Yankin Attawa, Tammawa, Dika, Gulu, Rimin Gado da kuma Jilli da ke cikin Rimin Gado.
Dazu Jaridar Punch ta rahoto cewa Jami’an tsaro sun kuma yi nasarar cafke wani da aka samu da yunkurin sace kayan zabe a akwatin Gama da ke cikin karamar hukumar Hukumar Nasarawa.
A wasu wurare kuma dai ‘yan daba ne su ka zagaye harabar zaben inda su ka hana kowa kada kuri’u. Mu na samun rahotanni cewa ‘yan iskan gari sun dangwale kaf kuri’un wasu Mazabun.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng