Zagaye na biyu: Dan takarar dan majalisa a APC ya janye, ya koma PDP

Zagaye na biyu: Dan takarar dan majalisa a APC ya janye, ya koma PDP

Wani dan takarar kujerar dan majalisar jiha a karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a zagaye na biyu na zaben da ake yi yau a mazabar Ezza ta Arewa, jihar Ebonyi mai suna Mista Innocent Nomeh ya janye takarar sa, ya kuma koma jam'iyyar PDP.

Majiyar mu ta kamfanin dillacin labarai ya ruwaito mana cewa zaben na raba gardama a ranar 9 ga watan Maris ne aka sa za'a yi shi amma sai 'yan daba suka tada rikici kuma sakamakon hakan har zaben ya ki wakana har sai da aka sake saka ranar 23 ga Maris.

Zagaye na biyu: Dan takarar dan majalisa a APC ya janye, ya koma PDP
Zagaye na biyu: Dan takarar dan majalisa a APC ya janye, ya koma PDP
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: An kama wani jigon PDP a filin jirgi

Mista Nomeh ya bayyana hakan ne a wata fira da yayi da manema labarai a garin Abakalki, babban birnin jihar na Ebonyi jim kadan bayan sanar da janyewar sa daga takarar saboda abun da ya kira kunnen uwar shegu da uwar jam'iyyar su da shugaban kasa da dan takarar gwamnan jihar.

A wani labarin kuma, Yayin da daukacin 'yan Najeriya ke cigaba da dakun mutanen da Shugaba Muhammadu Buhari zai nada matsayin ministoci a zabgon wa'adin mulkin sa na biyu, wata kungiya ta musulmai dake rajin kare hakkin musulmai musamman ma a yankin kasar Yarbawa ta bukaci ya ba su wasu kujeru.

Kungiyar ta Muslim Rights Concern (MURIC) a takaice ta bayyana wannan matsayar ta ta ne a cikin wata takardar da suka aike ga shugaban kasar dauke da sannun shugaban ta ranar Juma'ar, Farfesa Ishaq Akintola.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel