Zabe: Ku fito ku zabi wadanda ku ke ra'ayi: Sakon Buhari ga 'yan Najeriya

Zabe: Ku fito ku zabi wadanda ku ke ra'ayi: Sakon Buhari ga 'yan Najeriya

A daren jiya Juma'a ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci 'yan Najeriya su fito kwansu da kwarkwata domin kada kuri'un su a zabukan da za a gudanar a wasu jihohi.

Za a gudanar da zabukan ne a jihohi 17 ciki har da zabukan gwamnoni da za a kammala.

Shugaban kasa ya karyata rahoton da ke cewa yana kokarin ganin wasu 'yan takara da ya ke goyon baya sun lashe zabe ta kowane hali.

A sakon da ya fitar ta hannun hadiminsa na fanin kafafen watsa labarai, Garba Shehu, Shugaban kasa ya yiwa 'yan Najeriya godiya saboda sake zabensa da su kayi.

DUBA WANNAN: Sule Lamido ya fadi yadda APC da Kwamishinan 'yan sanda suka yiwa PDP magudin zabe

Zabe: Ku fito ku zabi wadanda ku ke ra'ayi: Sakon Buhari ga 'yan Najeriya
Zabe: Ku fito ku zabi wadanda ku ke ra'ayi: Sakon Buhari ga 'yan Najeriya
Asali: Twitter

Ya ce, "Nayi matukar murna bisa amanar da kuka danka min, ba zan taba cin amanarku ba. Ina muku godiya bisa goyon bayan da kuke bani."

A game da zabukan yau Asabar, Buhari ya ce, "Zabukan suna da muhimmanci kamar wadanda akayi kafin su."

A kan jita-jitar da ake yadawa na cewa yana tilasta wasu 'yan takara a kan al'umma, shugaban kasan ya ce wannan ba gaskiya bane kuma ya yi kira ga 'yan Najeriya su zabi wadanda suke so.

Ya kara da cewa, "Nayi imani da abinda al'umma ke so saboda haka ba zan tilastawa masu zabe wanda ba su kauna ba."

Shugaban kasan ya yi amfani damar wurin kira ga Hukumar Zabe INEC da sauran hukumomin tsaro su tabbatar anyi zaben lafiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel