Gwamnati tayi maza-maza ta bada kyautar filaye ga masu aikin zaben Jihar Kano

Gwamnati tayi maza-maza ta bada kyautar filaye ga masu aikin zaben Jihar Kano

Daily Nigerian ta rahoto cewa Mai girma gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje, ya bada umarnin cewa ayi maza a rabawa wasu ma’aikatan hukumar zabe watau INEC kyautan filaye a Kano.

Jaridar ra rahoto daga Majiya mai karfi cewa gwamnan ya bada umarni a bada kyautar filaye ne ga manyan Jami’an hukumar INEC a lokacin da ake shirin gudanar da zaben gwamnonin jihohi a cikin farkon watan nan na Maris.

Wasu takardu da ke hannun Daily Nigerian sun nuna yadda gwamna Abdullahi Ganduje ya umarci babban Sakataren din-din-din na hukumar da ke kula da harkokin filaye a Kano ya bada kyautar wadannan filaye da ke cikin Birni.

KU KARANTA: ‘Yan Kwankwasiyya sun ajiye jar hula sai bayan zaben Kano

Gwamnati tayi maza-maza ta bada kyautar filaye ga masu aikin zaben Jihar Kano
Gwamnatin Kano ta nemi a rabawa Jami'an zabe kyautar filaye
Asali: Facebook

Gwamnan da kan-sa ya nemi Muhammad Yusuf-Danduwa ya rabawa manyan ma’aikatan hukumar INEC fegin filayen ne kafin a gudanar da zaben gwamna a jihar. Har yanzu dai gwamnatin Kano tayi gum game da wannan zargi da ake yi.

Gwamnatin jihar za ta rabawa Malaman zaben filayen ne daga cikin Unguwar Umarawa da irin su Bandirowa kamar yadda gwamnan ya rattaba hannu tuni. Kwamishinan INEC yace za suyi bincike game da wannnan lamari kwanan nan.

Yanzu haka gwamna Ganduje da kan-sa ne ke rike da mukamin Kwamishinan harkokin filaye tun bayan da aka hada ma’aikatar filaye da kuma hukumar KANGIS ta jihar Kano a wuri guda. A yau ne kuma ake sa ran karasa zaben Jihar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel