Da dumin sa: Jami'an tsaro sun cafke jigon PDP, shugaban kamfanin AIT a filin jirgi

Da dumin sa: Jami'an tsaro sun cafke jigon PDP, shugaban kamfanin AIT a filin jirgi

Jami'an tsaro a filin sauka da tashin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe na kasa-da-kasa, garin Abuja sun cafke shugaban kamfanin yada labarai na AIT da Ray Power, Mista Raymond Dokpesi yana dawowa daga kasar Dubai inda yake neman lafiya.

Gidan Talabijin din AIT ne dai ya sanar da hakan inda suka ce daya daga cikin jami'an hana shige da fice ta kasa watau yace umurni ne suka samu daga sama na cewa su kama shi da ya dawo Najeriya.

Da dumin sa: Jami'an tsaro sun cafke jigon PDP, shugaban kamfanin AIT a filin jirgi
Da dumin sa: Jami'an tsaro sun cafke jigon PDP, shugaban kamfanin AIT a filin jirgi
Asali: Getty Images

KU KARANTA: Magudi: INEC ta maidawa Amurka kakkausan maratani

Shi dai Mista Dokpesi yana fuskantar tuhuma ne akan zargin hadin baki da wasu wajen karkatar da kudaden da aka ware don siyen makamai da suka kai Naira biliyan biyu daga ofishin mataimaki na musamman kan tsaro na tsohon shugaban kasa Jonathan, watau Sambo Dasuki.

A wani labarin kuma, Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya bayar da karin haske akan irin gwamnatin da zai yi wa'adin sa na biyu inda yace zai gudanar da gwamnatin sa ne a faifai kuma wadda zata tabbatar da adalci ga kowa.

Haka ma dai shugaban kasar wanda ya doke dan takarar jam'iyyar PDP a zaben shugaban kasar da ya gabata, ya ce wa'adin mulkin sa zai mayar da hankali sosai a fannin tsaro da kuma farfado da tattalin arzikin kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel