Na rigaya da daukaka kara - Gwamnan jihar Osun

Na rigaya da daukaka kara - Gwamnan jihar Osun

Gwamnan jihar Osun, Gboyega Oyetola, ya bayyana cewa tuni ya daukaka karar hukuncin kotun zabe da ta koreshi daga kujerar gwamnansa a ranar Juma'a, 22 ga watan Maris, 2019.

Oyetola wanda ya bayyana hakan a jawabin da sakataren gwamnatin jihar, Mista Wole Oyebamiji, ya saki a birnin Osogbo, ya ce za su samu adalci.

Jawabin yace: "Gwamnatin jihar Osun tana matukar godiya bisa ga goyon bayan da yawancin mutan jihar ke yi mata."

"A yanzu haka, mai girma gwamnan jihar Osun, Adegboyega Adetola, yana tabbatarwa jama'a cewa ya daukaka karar hukuncin kotun zabe."

" Muna kara tabbatarwa mutan jihar cewa tsaron rayukarsu da dukiyoyinsu da yake hakkin gwamnati ne, har yanzu yana hannunmu. Muna tabbatar muku da cewa za'a samu adalci dagakarshe. Kuma mun umurci jami'an tsaro su tabbatar da doka da oda."

"Saboda haka muna kira ga jama'ar jihar su fita ayyukansu na yau da kullum ba tare da wani cikas ba."

Mun kawo muku rahoton cewa kotun da ke sauraron korafe korafen zaben gwamnan jihar Osun da ke da zama a babban birnnin tarayya Abuja ta bayyana jam'iyyar PDP da dan takararta a zaben gwamnan jihar da aka gudanar a shekarar 2018, Sanata Ademola Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.

Kotun ta kuma yanke hukuncin cewa ba jam'iyyar APC da dan takararta, Gboyega Oyetola ba ne suka lashe zaben, don haka ta kwace nasarar da aka baiwa jam'iyyar bayan zaben jihar zagaye na biyu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel