Sama da mutane 3.5 milyan na bukatar tsabtacaccen ruwa a Najeriya - UN

Sama da mutane 3.5 milyan na bukatar tsabtacaccen ruwa a Najeriya - UN

- Bincike ya nuna cewa sama da mutane miliyan uku da rabi ne suke amfani da ruwa marar tsabta a Najeriya, musamman a yankin Arewa maso Gabas

- UNICEF tace zata yi bakin kokarin ta wurin samar wa da mutane tsabtacaccen muhalli.

Hukumar UNICEF ta bayyana cewa sama da mutane miliyan uku da rabi ne suke bukatar tsabtacaccen ruwa a Najeriya.

Hukumar tace wani jami’inta ne dake kasar mai suna Muhammed Fall, ya bayyana hakan a yau juma’ar nan, a lokacin da aka taron murnar ranar ruwa ta dunya.

Mista Fall, ya bayyana mutane sama da miliyan daya wadanda rikice-rikice ya raba su da gidajen su, wadanda da yawa daga cikin su suke fama da wannan matsalar ta rashin tsabtacaccen mahalli da wurin zama.

KU KARANTA: Hukumar EFCC ta kama wani da laifin sayen kuri’u

Ya ce kusan mutane 800,000 ne suke cikin wannan hali wanda kashi 79 cikin 100 yara ne da mata.

A Najeriyan dai matsalar tsaro ta shafi mutane da dama musamman ma wadanda suke zaune a yankin arewa maso gashin kasar, wanda hakan ya jawo musu zama a muhalli marar tsabta, da kuma yin amfani da ruwa gurbatacce.

A shekarar 2017 sama da mutane 5,365 sun kamu da cutar Amai da Gudawa, inda mutane 12,643 suka kamu a shekarar 2018, daga ciki mutane 175 sun rasa rayukan su ta sanadiyyar cutar.

Shugaban hukumar ta UNICEF, Henrietta Fore ya bayyana cewa matsalar rashin tsaron ta fi shafar yara wadanda suke kasa da shekaru 15, sannan kuma akwai yiwuwar kamuwar cutar ta Amai da Gudawa, sabida rashin tsabatacaccen ruwa da muhalli.

Shugabar hukumar ya bayyana cewa hukumar tasu zata yi iya bakin kokarinta wurin ganin sun bada taimako musamman ga sansanin ‘yan gudun hijira, domin tabbatar da tsabtacaccen muhalli ga mazauna wurin.

Sannan kuma ta kara bayyana cewa hukumar tana iya bakin kokarin ta wurin ganin ta rage cututtukan da suke damun al’ummar yankunan da abin ya shafa.

A karshe ta bayyana cewa ana samun matsalolin ne ta dalilin hare-hare da ake kaiwa yankunan da abin ya shafa, inda da gangan ake bata hanyoyin magudanan ruwa sabida a sanya mutane cikin halin kaka na kayi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel