Hukumar EFCC ta kama wani da laifin sayen kuri’u

Hukumar EFCC ta kama wani da laifin sayen kuri’u

- A dai dai lokacin da hukumar INEC ta ke tsawatarwa akan masu magudin zabe, sai gashi an kama wani dumu-dumu da laifin sayen kuri’a

- Sai dai wani lauya ya bukaci kotu ta bada belin mai lafin

A jiya ne hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya (EFCC) ta gurfanar da wani mutum mai suna Abdulsalam Abdulkadiri, a babbar kotun Ilorin dake jihar Kwara, inda ake zargin shi da hada baki da wani mai suna Oye Obalola domin ya bayar da naira dubu 120 domin yin amfani da kudin wurin sayen kuri’u ga wata jam’iyya.

Har ya zuwa yanzu dai ba a san inda Obalola yake ba, inda a halin yanzu ake zargin Abdulkadiri da bada naira dubu 120 domin amfani dasu a mazaba mai lamba 007 dake makarantar kwalejin ilimi dake jihar ta kwara.

A lokacin da yake bayani, daya daga cikin jami’an hukumar ta EFCC, Nnemka Omewa, ta ce kotu ta dauki kwakwaran mataki akan mai lafin.

Sai dai kuma mai kare mai laifin O.S Mohammed ya bukaci kotu tayi wa mai laifin sassauci, sannan ya bukaci kotu ta bayar da belin Abdulkadiri.

KU KARANTA: An jefar da jariri da wasika mai sosa zuciya a garin Kaduna

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel